Yaya kasar Sin take a sabon zamani? Jerin shirye-shiryen da babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice ya shirya kwanan baya, dangane da “Kasar Sin a Sabon Zamani” irin su “Yadda kasar Sin take a shekaru goma da suka wuce”, da “Labarun kasar Sin a idona”, da “hanyar samun wadata tare”, sun ba ku labaran abubuwan da suka faru a kasar Sin cikin shekaru goma da suka gabata.
Baya ga shirye-shiryen da aka ambata a baya, an kaddamar da “bikin bidiyo na kasar Sin”, wanda CMG da ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin suka shirya a hukumance, a kwanaki kadan da suka gabata. Ya zuwa yanzu, gidajen talabijin, da cibiyoyi na ketare guda 30, daga kasashen Afirka 20 ne suka halarci wannan baje kolin, kuma za a nuna shirye-shiryen bincike masu inganci na kasar Sin fiye da 50, wanda gidan talabijin na CGTN, dake karkashin jagorancin CMG ya shirya a kasashen ketare daya bayan daya, wanda hakan ke haskaka gaskiyar kasar Sin a dukkan fannoni ga abokai na Afirka. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp