Tun daga ranar 12 ga wannan wata, Sin ta fara karbar kaso 125 bisa dari na harajin fito kan kayayyakin Amurka da ake shigarwa kasar, a matsayin martani ga manufar “ramuwar gayya” da kasar Amurka ta nunawa kasar Sin. Hakazalika kuma, bangaren kasar Sin ya yi bayani a gun taron shekara-shekara na farko na majalisar cinikayyar kayayyaki ta hukumar WTO cewa, ramuwar gayya tana bukatar bangarorin da suke yin ciniki su samarwa juna sauki da moriya cikin adalci bisa ka’idojin WTO, ta yadda za su samu moriyar juna a karshe. Sai dai sabanin haka, manufar “ramuwar gayya” ta kasar Amurka tana nufin ra’ayin bangare daya, da samun moriyar kanta kadai, wanda hakan mataki ne na cin zarafin tattalin arziki.
Gwamnatin kasar Amurka ta kyale hukumar WTO da dokokinta, tana aiwatar da manufar “ramuwar gayya”, wadda ta sabawa ka’idar WTO ta samar da gata ga wasu kasashen duniya, bisa tushen nuna adalci ga dukkan kasashen duniya da dai sauran ka’idojin WTO.
- Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?
- Sin Ta Yi Allah-wadai Da Karin Harajin Amurka Ta Kuma Jaddada Goyon Bayanta Ga Ka’idojin WTO
Kana maganar da kasar Amurka ta yi cewar ana yi mata illa a yayin cinikayya, ta hanyar harajin kwastam ba adalci a ciki, kuma ba ta da tushe. Kudin Amurka kudi ne na duniya, kuma kasar Amurka tana iya yin amfani da kudinta wajen samun wadata a duniya. Lokacin da kasashe abokan cinikayya suka yi kokarin samar da kaya, kasar Amurka tana iya samun moriya ta hanyar kara fitar da kudinta. Wannan ya shaida cewa, ko da kasar Amurka ta fuskanci gibin ciniki, a daya hannun tana iya samun kayayyaki masu inganci daga kasashen duniya. Hakika tana samun moriya daga sassan kasa da kasa.
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp