Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya aurar da wasu ‘ya’yansa biyar bayan darewa kan karagar mulki, tun daga 2016 zuwa 2022.
Ga jerin sunayen ‘ya’yan nasa da aurar da mazajensu:
- Matsin Lamba: Shugaban Kasar Sri Lanka Zai Yi Murabus
- Buhari Ya Jinjina Wa Masu NYSC Kan Gyara Rijiyoyin Burtsatse A Daura
1. Suna: Fatima Buhari da Gimba Kumo
Ranar Aure: Oktoba 2016
Sadaki: 100,000

2. Suna: Zahra Buhari da Ahmed Indimi
Ranar Daurin Aure: 16 ga watan Disamba 2016
Sadaki: N250,000

3. Suna: Hanan Buhari da Turad Sani Sha’aban.
Ranar daurin aure: 4 ga watan Satumba, 2020
Sadaki: Ba a bayyana ba

4. Suna: Yusuf Buhari da Zahra Nasir Bayero
Ranar aure: 20 ga watan Agusta 2021
Sadaki: N500,000

5. Suna: Hadiza Buhari da Abubakar Malami
Ranar aure: 8 ga watan Yuli, 2022

Sadaki: Babu tabbacin abin da ya biya a matsayin sadaki, amma ana zargin ya biya Naira miliyan 100 sannan ya ba ta kyautar gida a Maitama Abuja da wasu manyan motoci guda biyu.
Wadannan sune jerin sunayen ‘ya’yan shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya aurar tun bayan zama shugaban kasar Nijeriya a 2015, sannan ya sake maimaitawa a 2019.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp