Fara yakin neman zabe a tsakiyar makon nan ya kasance tubulin ginin sauya ragamar mulki daga hannun gwamnatin mai ci ta Shugaba Muhammadu Buhari zuwa wata da ‘yan Nijeriya za su zaba a shekarar 2023.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a cikin jadawalin da ta yi na zaben 2023, ta kebe ranar 28 ga watan Satumbar 2022 domin fara yakin neman zabe ga ‘yan takarar shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya, yayin da ‘yan makwanni bayan nan su ma masu gogoriyon neman kujerun gwamnoni za su fita fagen fama tare da ‘yan takarar kujerun majalisun dokoki na jihohi.
- Tsare-tsaren CBN Don Samar Da Kyakkyawar Alkibla Ga Tattalin Arzikin Nijeriya
- ‘Yan Kannywood Sun Nuna Alhinin Rasuwar Jarumi Umar Yahaya Malumfashi
•An Fara Ba Tare Da Warware Rikicin Jam’iyyu Ba
Sai dai kuma an fara gudanar da yakin neman zaben na 2023 a hukumance ne ba tare da warware rikicin cikin gida da jam’iyyun siyasa ke fama da su ba. Yakin neman zaben shi zai bai wa ‘yan takara damar tallata kansu wajen gabatar wa masu jefa kuri’a manufofin da suke son cimmawa a lokacin da suka hau kan karagar mulki. Ga dukkan alamu wani sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar APC lokacin da aka fitar da sunayen kwamitin yakin neman zabe a makon da ya gabata.
Inda kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya nesanta kansa da sunayen da aka fitar saboda a cewarsa ba a shawarce shi ba. Wani dan kwamitin gudanarwar ya tabbatar da cewa akwai kurakurai da dama a cikin sunaye, domin ba duka shugabannin jam’iyyar suka amince da su sunayen ba.
Abu na farko da ake tunanin ya fara tayar da kura, shi ne rashin ganin sunan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a cikin kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu ba. Lamarin da ya raba kan ‘ya’yan jam’iyyar, inda wasu ke ganin cewa an mayar da wasu saniyar ware.
Masu sharhin al’amuran siyasa na ganin cewa matukar jam’iyyar ba ta yi kokarin lalubo hanyar warware matsalar Kafin zabe ba, to karamar magana za ta zama babba.
A bangaren jam’iyyar PDP kuwa, lamarin bai sauya zani ba. Inda har yanzu jam’iyyar take faman lalubo hanyar warware rikicin da ke tsakanin Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da jam’iyyar. Rikicin PDP ya kara yin kamari ne lokaci da Wike ya bukaci sai shugaban PDP, Ayorchia Ayu ya sauka daga kan mukaminsa.
Tun dai bayan kamala zaben fid da gwani a PDP da zaben gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin takarar Atiku aka fara samun takun-saka tsakanin Wike da Atiku. Duk da kokarin da jam’iyyar take yi wajen sulhunta Wike da Atiku amma lamarin ya ci tura.
Inda ko a cikin wannan makon, magoya bayan gwamnan Jihar Ribas suka ci gaba da dagewa sai shugaban jam’iyyar ya sauka daga kan mukaminsa. A cewarsu, an yi alkawarin
Ayu zai sauka daga mukaminsa idan aka samu dan takara daga yankin arewa a karkashin jam’iyyar PDP, amma a yanzu sai aka kasa cika wannan alkawari.
Da yake zantawa da shafin LEADERSHIP na Tuwita, mashawarcin Wike kan kafafen sadarwa, Marshal Obuzor ya bayyana cewa ba za su taba goyon bayan Atiku ba har sai Ayu ya sauka daga kan mukaminsa domin cika alkawarin da aka yi a baya. Obuzor ya kara da cewa PDP ba za ta taba samun nasara a zaben 2023 ba in har ba ta hada kan ‘ya’yanta ba.
Har ila yau, bayan APC da PDP, ita ma jam’iyyar LP da ake ganin ta fito da karfinta a zaben da za a gwabza na 2023, tana fama da rarrabuwar kawua, inda wasu magoya bayan jam’iyyar suke bayyana cewa shugabancin jam’iyyar bai da maraba da na PDP da APC.
Haka ma lamarin yake a cikin jam’iyyar NNPP, wanda aka samu rikicin shugabancin da ya yi sanadiyyar ficewar tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau zuwa PDP. Shekarau dai ya ce rashin adalcin da aka yi wa bangarensa ne ya kore shi daga jam’iyyar, kuma ga dukkan alamu ba zai yi kwanare ba duk da INEC ta kafe kai da fata cewa ba ta san wani dan takarar NNPP a mazabar Kano ta tsakiya ta Sanata ba sai Shekarau.
Kowacce jam’iyya dai na fama da irin nata matsalolin na cikin gida wanda galibin masu fashin baki na ganin matukar ba su warware ba, lamarin na iya yi musu kancal a zaben na 2023.
• Sharuddan Da Dattawan Arewa Suka Gindaya
A bangaren al’umma kuwa, yayin da aka fara yakin neman zaben, Kungiyar Dattawan Arewa ta NEF, ta gindaya wa ‘yan takarar shugaban kasa dabandaban sharuddan da za su cika kafin su sami kuri’un yankin arewa. Kungiyar ta yi ikirarin cewa a yankin arewa ba za a yi zabe don addini ko kabilanci ba, wanda zai iya gyara Nijeriya ne kadai zai samu kuri’un yankin.
Kungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunta, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ga ‘yan jarida a farkon makon nan.
Baba-Ahmed ya kara da cewa dattawan arewan sun tabka babban kuskure a 2015 lokacin da suka bukaci mutane su zabi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba tare da sanin manufarsa ba.
Ya ce, “Za mu tattauna da dukkan ‘yan takara ciki har da Atiku, Tinubu, Obi da Kwankwaso domin jin manufofinsu tare da fitar da wanda ya fi dacewa, saboda mu ne ke dauke da alhaki a kansu wajen shawartar mutanen arewa alkiblar da za su bi.
“Abin da muka yi alkawari a wannan lokaci shi ne, ba za mu maimaita kuskuren da muka tafka a 2015 na cewa a zabi Baba Buhari kadai ba, kuma lokacin da ya hau kan karagar mulki ya kasa gudanar da abubuwan da ya kamata ya yi.
“Mun yi wa Buhari yakin neman zabe a 2015 da 2019, a yanzu ya gaza kuma babu sauranlLokacin gyarawa. A yanzu muna neman ci gaban kasa ne. Ba za mu sake yin wani kuskure ba.” Lokacin da aka tambaye shi ko daya daga cikin ‘yan takara na yankin arewa zai kasance daga cikin sharuddan, ya bayyana cewa babu wannan maganar, za su mara wa dan takarar da ya cancanta ne kadai.
“A wannan lokaci zabinmu a bayyana yake. Ba za mu yi zabe saboda bangaren da dan takara ya fito ba. Ina wannan maganar a madadin dukkan ‘yan kungiyar dattawan arewa. Ba hujja ba ce mu ce sai dan takarar da ya fito daga arewa za mu zaba. Ba mu ware ‘yan arewa kadai ba, muna duba sauran ‘yan takara da suka fito daga ko’ina a sassan Nijeriya.
“Ban dai san abubuwan da sauran bangarorin kasa ke yi ba, amma mu a arewa ba za mu zabi duk wani dan takara ba har sai mun kammala cikakken binciken abubuwan da zai yi wa kasar nan,” in ji shi.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) dai ta ce jam’iyyu 18 ne za su shiga zaben da za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
• Zunzurutun Kudin Da Ake Sa Ran Kashewa
Ana ganin wadannan jam’iyyun za su kashe zunzurutun kudade wajen gudanar da harkokinsu na yakin neman zabe da kuma lokacin gudanar da zaben kansa. Sashi na 88 (2) na dokar zabe ta shekarar 2022, ya yi tanadin cewa karancin abin da dan takarar shugaban kasa zai kashe kar ya wuce naira biliyan biyar, yayin da karamin sashe na 9 ya yi bayyana cewa duk dan takarar da ya saba wa sashin, ya yi laifi kuma za a hukunta shi kan duk kashi daya na yawan kudaden da ya kashe lokacin yakin neman zabe, inda za a daure shi a gidan yari na tsawan wata 12 ko kuma a ci tararsa.
Sai dai ana ganin Naira Biliyan 5 da aka kayyade ba mai yiwuwa ba ce, tare da has ashen cewa wasu ‘yan takarar za su narka abin da zai kai kimanin Naira Biliyan 100, domin ko alawus da za a baiwa wakilan jam’iyyu a rumfunan zabe zai kai akalla Naira Biliyan 3.5.
Idan dai za a iya tunawa a 2019 an kayyade yawan kudin da dan takarar shugaban kasa zai kashe a kan naira biliyan 1.
Amma a yanzu an mayar da shi zuwa biliyan biyar sakamakon gyaran fuska da majalisar kasa ta yi wa dokar zabe. Ana sa ran ‘yan takarar za su kashe kudaden ne wajen gudanar da gangamin zabe a jihohi dat tallace-tallace da sufuri da tsaro da janyo ra’ayoyin jama’a kan a zabe su.
• Alkawuran ‘Karya’ Da Ake Yi Tun Daga 2014 – Mai Sharhi
Wani mai sharhi kan al’amuran siyasa, Malam Nurudeen Dauda ya lassafto abubuwan da suka kamata ‘yan Nijeriya su lura da su a yayin yakin neman zaben na 2023, wanda zai dauki tsawan kwana 150 ana yi kafin gudanar da babban zabe.
“A nawa binciken, dukkan yakin neman zabenmu tun daga 2014 har zuwa yau, a kowani mataki ana gudanar da shi ne a bisa alkawuran karya, batanci da kuma tashin hankali, maimakon magance matsaloli. Bugu da kari, ana amfani da addini, bangaranci, kabilanci, shekaru, takardu, duk su suke dabaibaiye ‘yan takarar jam’iyyunmu.
Yakin neman zabenmu ya ta’allaka ne wajen bata suna da kalamun batanci a tsakanin ‘yan siyasarmu.
“Wasu daga cikin ‘yan jarida wadanda ya kamata su sauya alkiblar yakin neman zabe wajen magance matsalolin da ake fuskanta, sai suka kara ruruta wutar lamarin tare da hana kasarmu ci gaba. Akwai bukatar mahukunta su taka muhimmiyar rawa wajen hukunta wadanda aka samu da laifin karya ka’idojin yakin neman zabe.
“Ko shakka babu rashin tsaro da hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da talauci su ne manyan matsaloli da suka yi wa harkokin shugabanci katutu a Nijeriya. Wadannan matsaloli ba a bambance su a tsakanin ‘yan Nijeriya ko dai ta bangaren addini ko bangarenci ko kabilanci.
“Masu zabenmu a kowani mataki suna damuwa ne da kudaden da ‘yan takara suke ba su, akwai bukatar masu jefa kuri’a su dinga la’akari da abubuwan da za su daidaita harkokin shugabancin kasa.
“A nawa ra’ayi, muna bukatar shugabanni wadanda suke da tarihin magance matsalolin irin su rashin tsaro, hauhawar farashi, rashin aikin yi da kuma talauci ba tare da la’akari da bambanci a tsakanin ‘yan Nijeriya ba.
“Muna bukatar ‘yan siyasar da za su magance mana matsalolin da suka addabe mu. Lokaci ya yi da za mu kalubanci duk wani dan takara a kowani mataki wajen bayyana mana tsare-tsarensa, shiryesirye da manufofinsa idan mun zabe shi. Dole ne mu tambayi ‘yan siyasarmu su fada mana abubuwan da za su yi mana idan suka samu nasara domin mu iya bambance tsakaninsu.
“Domin daidaita al’amura, dole ne mu daina zabe bisa bangarenci ko kabilanci. Ya kamata mu yi la’akari da abubuwan da ‘yan siyasa suka yi lokacin da suke rike da mukaman siyasa ko matsayin aikin gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu ko kasuwancin da suke gudanarwa kafin mu zabe su.” Ya bayyana.
• Adadin Masu Zabe Ya Karu Da Miliyan 12.29
Bayanan da hukumar INEC ta fitar na nuna cewa an samu karin adadin masu zabe wadanda suka yi rajista mutum miliyan 12.29. A cikin wannan adadi, mutum miliyan 3.44 sun yi rajitar ne ta intanet, yayin da mutum miliyan 8.85 suka yi rajistar a zahirance. Inda yawan wadanda za su jefa kuri’a a zaben na 2023 ya kai mutum miliyan 96.3.
A bayanan da INEC ta wallafa na sabbin wadanda suka yi rajista, Jihar Legas ce ta fi yawan masu jefa kuri’a yayin da jihohin Ekiti, Yobe, da Abuja suke na kasa a wurin yawan wadanda suka yi rajistar zabe.
Kamar yadda kididdigar sabuwar rajistar zaben ta nuna, daga cikin mutum miliyan 12.29, akwai mata miliyan 6.22, wanda suka kai kashi 50.6%, yayin da miliyan 6.07 kuma suka kasance maza, da ke nuna kashi 49.4%.
Wakazalika, a cikin adadin sabbin rajistar miliyan 12.29, matasa ne ke da kaso mafi tsoka, inda suka kwashe kashi 71.4% wanda ya kai adadin miliyan 8.78.
Wannan ya nuna cewa a duk kashi 10 na yawan masu rajistar, kashi 7 matasa ne ‘yan shekara 18 zuwa 34. Kashi 7.8% dattawa ne ‘yan shekaru 50 zuwa 69, yayin da kashi 1.0% dattawa ne da suka kai shekaru 70, matasa masu matsakaitan shukaru ‘yan shekara 35 zuwa 49 sun kai kashi 19.8%.
• Kiraye-kirayen Shugabanni Kan Zaman Lafiya
A daidai lokacin da aka fara gudanar da yakin neman zaben na 2023, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Mohammed Sa’ad Abubakar da shugaban kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN), Daniel Okoh, sun yi kira da shugabannin addini da dukkan ‘yan Nijeriya su kiyaye furta kalaman da za su tarwatsa kasar nan.
Jagororin addinin sun bayyana hakan ne lokacin da suke jawabi a wurin taron zaman lafiya na addinai da ya gudana a Jihar Legas. Sun bayyana cewa yana da matukar muhimmanci su yi wannan kira adaidai lokacin da aka fara yakin neman zabe.
Taron da aka yi masa lakabi da ‘Aiki tare domin kawo zaman lafiya’ ya samu halartar sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha da gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu.
A nasa bangaren, Sarkin Musulmi ya ce shugabannin addini suna taka muhimmiyar rawa wajen kira ga mutane kan tafarkin gaskiya. Ya bukaci musulmai da kiristocin kasar nan da su hada kai domin samun zaman lafiya mai dorewa. A cikin jawabinsa, shugaban CAN, Okoh ya yi kira ga mutane da su zauna lafiya tare da kauce wa kalamun da ka iya tarwatsa zaman lafiya da kuma zaben shugabanni da suka dace a 2023 ba tare da la’akari da kabilanci ko addini ba.
Wakazalika, Kungiyar Tabbatar Da Zaman Lafiya bisa jagorancin tsohon Shugaban Kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ta nanata kiraye-kirayenta ga daukacin ‘yan takara su yi wa Allah da Manzonsa su mayar da hankali a kan batutuwan gyara kasa mai makon zagezage da kalaman batanci da za su tayar da zaune tsaye.
Kungiyar, kamar yadda ta tsara rattaba hannu a takardar yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa a ranar Alhamis 29 ga Satumbar 2022 ta ayyana cewa, dukkan ‘yan kasa sun san ba mu da wata kasa kamar Nijeriya, don haka a guje wa abin da zai iya sanadin shafe kasar ta zama tarihi.
Yanzu dai da yakin neman zaben ya kankama, za a iya cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.