Babban abin da dan kasuwa ya kamata ya rinka yi don ya yi maganin mantuwa shi ne zama mai tsara abubuwa a kullum.
Kuma yadda mutum zai tsara ayyukansa na yau da kullum shi ne; duk sanda mutum ya tashi daga barci bayan ya gama duk abin da ya kamata ya yi kafin ya fita ya zauna ya samu takarda da abin rubutu ya rubuta duk abin da zai yi a wannan ranar.
- Kammala aikin tashar ruwa mai zurfi ta Lagos zai ingiza bunkasar tattalin arzikin Najeriya
- Ana Jimamin Mutuwar Sarauniyar Giwaye Mai Shekara 65 A Kenya
Misali idan ka fita kasuwa bayan ka je me za ka yi,? Mu dauka bayan ka je kasuwar za ka fita zuwa wata kasuwar ka sayo wasu kaya, ko za ka ba wa wani kudi, ko kun yi alkawari da wasu za ku yi gana, ko za ka je banki ka karbo kudi ko ka kai. Idan an kula duk wadannan wasu hidimomi ne da za su iya taso maka ko kuma suna cikin huldarka ta yau da gobe.
Dalilin da ya sa ake so ka rubuta shi ne, in dai ka rubuta abubuwan da za ka yi a kowace rana babu wani abu da zai zo ya yi maka cikas, saboda ka tsara abubuwan da za ka yi a wannan ranar, sannan kuma babu wani da za ka aika wani wuri ya dawo bai yi ma bayani ba ka rabu da shi dalili kuwa shi ne, takardarka za ta tuna maka.
Sannan a lura duk sanda ka rubuta abubuwanka na yau da kullum wannan takardar ta zama tana tare da kai kamar yadda ake tare da kudinka a aljihu ita ma takardarka ko da yaushe tana aljihunka duk sanda ka gama wani aiki da ka rubuta a takardarka sai ka dauko takardar ka goge wannan aikin da aka yi. Misali ka rubuta yau idan ka zo kasuwa za ka ba wa wani kudi kuma sai ka sa wannan shi ne abin da za ka fara yi idan ka zo kasuwa, saboda haka kana zuwa idan ka bashi kudin sai kai maza ka dauko takardarka ka goge wannan aikin da karubuta na farko da za ka yi bayan ka zo kasuwa.
Ta yaya za ka tsara ayyukanka?
A kula da kyau wajen rubuta abubuwan da mutum zai yi a rana. Ga yadda samfurin yake na jadawalin tsare-tsaren yau da kullum. Farko za ka samu takarda da abin rubutu za ka rubuta kamar haka. (a kula wannan misali ne kawai saboda mutane sun bambamta ta al’adu da sauransu)
- Zan ba wa (wane) kudi a kasuwa.
- Zan je banki na kai kudi ko na karbo
- Zan ziyarci abokina a gidansa bayan na tashi daga kasuwa
A takaice wadannan su ne yadda ake tsara abubuwan yi saboda halin mantuwa. Mai karatu ka fahimta wannan misali ne kawai za ka iya samun kanka kana da abubuwan yi da yawa a rana ka ga a nan dole kana bukatar ka san me za ka yi daki-daki, sannan in ka gama wannan sai me.? Sannan kuma da yawa za’a ga akwai abubuwan da suke bukatar sakamako ko na ce amsa, misali a aiki, na biyu za ka je banki ko ka aiki yaranka wani wuri ya karbo wani abu ko ya kai wani abu ta yaya za ka san ya je ya kai wannan sakon ko ya kawo maka sakamakon aiken in kai mutum ne mai yawan mantuwa kamar Alhajinmu da na ba da labarinsa a kwanakin baya da suka wuce. Kaga a nan ta hanyar rubutu kawai za ka iya ganewa wannan aiken an je shi ko ba a je shi ba.
Sannan wani abu mai mahimmacin gaske shi ne a wani bangaren kana bukatar wata takardar ta biyu wacce za ta rinka lissafa maka abin da ka yi na kudi ko wani kaya da yake fita. Akula a nan takarda ta farko tana nusar da kai ne ta abubuwan da aka tsara za’a yi a rana, amma ita ta biyu za ta rinka nuna maka yadda wani abu ya fita ta bangarenka.
Misali a aiki na farko za ka ba wa wani kudi, binka ya ke yi ko kuma kyauta za ka yi masa? To a nan dole sai takardarka ta biyu ta nuna cewa Naira kaza sun fita ta dalili kaza, saboda in ka zo lissafi ka san inda wannan Naira kazan ta shiga, amma idan kawai ka rubuta na ba da kudi nawa ka bayar ba ka sani ba domin ka manta amma idan ka rubuta adadi baka da wata matsala balle ka fara zargin ana yi maka sata.
Ba zai yiwu ba mu zauna ko yaushe mu ce mu ba za mu yi tsarin rayuwarmu ba, saboda muma mutane ne kamar kowa. Don me mutumin Amerika zai yi tsari, mu ‘yan Afrika ko na ce ‘yan Nijeriya ba za mu yi ba? Ba fa fin mu suka yi ba, in an kula kasashen da ake gani sun ci gaba ba kawai lokaci guda suka ci gaba ba, sai da suka yi tsari tun daga cikin gidajensu sannan tsarin ya karade ko’ina. Dalilin haka ne ko hira muke yi ta yau da kullum idan za’a kawo misali sai a ce bature ma ga yadda yake yi, sai ka ga mun ba wa turawan nan wani fifiko na musamman, don me? Saboda suna da tsari, mu kuwa ba mu da shi.
Anan nake so na jawo hankalin ‘yanuwa mu daina hango wahala a cikin abubuwan da za su amfani rayuwarmu muna kin yi saboda kawai ba ma so mu sha wahala. Kuma a gaskiya ni ban ga abin wahala ba don kullum na tsara abin da zan yi a takarda na sa wannan takardar ta zama kullum tana tare da ni ya zama abin yin korafi. Da fatan don Allah za mu cire kiwa mu yi abin da ya dace da rayuwarmu.
Akwai wanda aka ba ni labarinsa a Kano bai fi shekara 27 ba amma ya kai shekara 10 yana rubuta duk abin da zai yi. Kuma wani abin mamaki ga wannan matashi shi ne tun dare yake zama kafin ya yi bacci ya rubuta abin da zai yi gobe in Allah ya wayi gari yana raye.
Wannnan matashin hatta idan zai je gurin budurwarsa zance sai ya rubuta zai je zance yau, sannan kuma sai ya rubuta iya lokacin da zai bata. Misali idan ya tsara zai yi minti 40 a wurinta to ba zai kara lokaci ba wannan minti 40 din ita zai yi, saboda tsarinsa abokansa suka sa masa suna ‘Tsari!
To amma wani abin sha’awa shi ne yana da tireda da yake sayar da kayayyaki irinsu; sikari, sabulu da sauran kayan masarufi. Saboda haka in dai ka zo ka ce ya baka bashin wani abu zai baka, amma sai ya dauko littafinsa ya duba ya ga nawa yake binka in kuma ba ya binka ya baka, sannan kuma dole sai ka sa masa hannu, ma’ana shaidar ka karba.
Yanzu yana nan da babban kanti a unguwa kuma yana zuwa makarantar gaba da sakandare. Karatunsa bai hana shi neman kudinsa ba, bai hana shi duk wasu abubuwa da yake so ya yi ba, dalili kuwa shi ne ya yi tsari me kyau game da rayuwarsa.