Duk da kiki-kaka da zaman tankiya da ake ci gaba da fuskanta tsakanin magoya bayan Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Lawan da bangaren Hon. Bashir Machina, kan takarar Sanatan Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC, hakan ba ta hana gudanar da gangamin yakin neman zaben ba.
Muhammed Dauda Sa’id (Gaskanta) shi ne Ko’odinatan yakin neman zaben dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa, Hon. Bashir Machina, inda ya bayyana wa wakilinmu a jihar Yobe cewa, duk da rashin fahimtar da wasu daga cikin magoya bayan Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Lawan suka yi wa al’amarin, amma hakan bai hana yakin neman zaben samun gagarumar tarba daga al’ummar yankin ba.
Ya ce, a tarukan da suka gudanar a kananan hukumomin Nguru, Karasuwa, Machina da Gashuwa, ya gudana cikin nasara tare da nuna goyon bayan dubun-dubatar jama’a. Ya ce wannan alamu ne da suka nuna al’ummar yankin suna cike da shaukin samun canjin sabon hannu don ya jagoranci Yobe ta Arewa zuwa ga samun ci gaba mai dorewa, bayan zaben 2023.
“Kuma a matsayina na Ko’odinatan yakin neman zaben sa, abin alfahari ne gareni bisa yawan jama’ar da suka fito maza da mata, yara da manya- jama’a ne ke tururuwa daga Ofishin Yan-sanda na bakin garin Gashuwa zuwa kofar Fadar Mai Bade; tazarar kilomita daya da digo biyar, sai da ya kwashe awanni biyu da minti 5 kafin ya isa Kofar Fada.
Saboda yadda jama’a ke daukin samun sabon canji.”
Hon. Gaskanta ya kara da cewa, wannan karbuwa da Hon. Bashir Machina yake samu alamun nasara ne, saboda dukanmu ya’yan jam’iyyar APC ne, kuma mutane ba a shirye suke su bar jam’iyyar ba, masu da’a da biyayya ne ga jam’iyyar APC. “Babu yadda za a yi irin wannan sabanin da aka samu ya hana cikakken dan jam’iyyar yaki zabar mutumin da jam’iyyar ta tsayar ba.
Sannan wannan rigimar bata yi tsamin irin wadda ta faru tsakanin marigayi Gwamna Mamman B. Ali da marigayi Sanata Usman Al-Bashir ba, saboda shi Sanata Ahmed Lawan bai yi takarar Sanatan Yobe ta Arewa ba, face kawai shugaban jam’iyyar APC na kasa ne yake neman ya kwace kujerar ya bashi.”
Ya kara da cewa, “Sannan kuma shi Shugaban jam’iyyar APC na kasa bai fito ta hanyar lalama ba, saboda mu ‘ya’ya ne, kanne, kuma iyaye a wata fuskar, kuma da ace an bukaci zama da Hon. Bashir Machina da mu magoya bayan sa, a nemi taimakonmu a lokacin da Sanata Ahmed Lawan ya fadi zaben fidda-gwani na Shugaban kasa, a nemi alfarmar a bar masa takarar Sanatan Yobe ta Arewa, wannan daidai ce. Amma ba ta nuna karfin shugabancin jam’iyya ba.” Ya nanata.
“Kuma matakin da Hon. Bashir Machina ya dauka na zuwa kotu daidai ne, saboda ba a nemeshi ta sulhu ba, sai ake neman ayi masa ‘ko da tsaiya-tsiya, ko da karfin tsiya’ ka ga dole ya garzaya inda za a kwata masa hakkinsa; inda mu mabiyansa muka goya masa baya har Allah ya bashi nasara a kotu karon farko da na biyu. Ko in Sha Allah yadda jama’a suka yi maraba dashi haka zasu jefa masa kuri’a cikin nasara.”
Ko’odinatan ya kara da cewa, kwamitin yakin neman zaben Hon. Bashir Machina suna kai-komo wajen lallashin magoya bayan Shugaban Majalisar Dattawan, suna binsu gida-gida tare da basu hakuri, ya ce, “Shima Sanata Ahmed Lawan zamu nada kwamiti mu sameshi har gida mu bashi hakuri.
Saboda dukanmu ya’yan jam’iyyar APC ne kuma a karkashin Limamin Sulhu, Hon. Mai Mala Buni, wanda kowa ya san matsayin sa na sulhunta ya’yan jam’iyyar APC a matakin kasa ba a Yobe kadai ba.”
A hannu guda kuma, Muhammed Dauda Sa’id ya kara da cewa, babban kuskure ne wani ya zargi Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni kan goyon bayan wani bangare ko nuna bambanci tsakani.
Ya ce rashin adalci ne a zargi Gwamna saboda shi uban kowa ne kuma babu wata hujja ko shaida a Kan hakan, face kawai zance ne maras tushe da makama. Ya ce, “Kowa ya san wanda ya haddasa mana wannan fitina ta cikin gida, ba kowa bane face Shugaban jam’iyyar APC na kasa.”
A karshe ya bayyana cewa, “Muna kira ga daukwacin al’ummar wannan yanki da jihar Yobe baki daya, kowa ya hakura a hada kai ayi abu guda kuma mu fuskanci ci gaban yankin mu da jiharmu dama kasa baki daya. Kuma muna kira ga matasanmu don Allah ayi hakuri a mutunta juna kuma a guji bangar siyasa a mutunta juna.
Sannan bama goyon bayan duk wani aiki ko kamalan cin zarafi da bayyana kiyayya ga junanumu, muna ba kowa hakuri azo ayi aiki tare.” Ya nanata.