Ana samun dinbin kudaden shiga masu yawa a fannin a kasar nan, musamman duba da yadda ake ci gaba da yadda wasu matasan kasar, ke ci gaba da fuskatar kangin matsin tattalin arziki, hakan ya tilastawa wasu matasan kasar, rungumar dabi’ar Caca, bisa nufin zamowa attajirai a dare daya.
Rahoto da Mujallar Lancet, ta wallafa, ta yi gargadin cewa, wannan dabi’ar na ci gaba da zama zamowa wata barazana ga fannin kiwon lafiyar masu yin dabi’ar a fadin duniya, musamman a Nijeriya, ganin yadda ake gudanar da wannan harkalar har a hanyar a wayoyin tafi da gidanka da kuma ta yanar Gizo.
Duba da cewa, masu yin wannan dabi’ar akasarinsu, su kan kasance a lokacin da suke kan gudanar da ita, suna yawan zukar Taba Sigari ko kuma yawan kwankawadar Barasa, saboda kara zurfin yin tunani, duba da cewa, masu yin dabi’ar da suka kai miliyan 450, za su iya fuskatar larurar ta kwakwalawa.
A saboda hakan ne, wasu kwararru, suka bayar da shawarar da a kakaba sharuddan kan yin tu’ammali da Taba Sigari da Barasa.
Bugu da kari, dangane da wani rahoto na alkaluman Statista na duniya da kuma sirrin gudanar da kasuwanci suka fitar, sun nuna cewa, kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 60, masu shekaru daga 18 zuwa 40, suka rungumi wannan dabi’ar.
Kazalika, a wani binciken kwanan baya na gama gari kan yawan alummar kasar, ya gano cewa, kaso 53 na wasu matasan kasar, a kullum suna rungumar wannan dabi’ar.
Sai dai, muna sane da cewa, wasu ‘yan Nijeriya, na kallon yin cacar tamkar wata aba ce, ta nishadi kawai, amma wasu bincike sun bayyana cewa, wani dan bangere na mutanen da ke yin cacar ne kawai, ke samun a cacar, inda akasarin sauran, ke tabka asarar kudadensu da suka zuba a cikin cacar.
An dai jima ana yin caca a kasar, wadda a shekarun baya, ake yi mata wani kallon kan abinda bai dace ba, kamar dai yadda Coci ta alakanta ta, a matsayin hanyar yin arzikin dare daya
Idan za a iya tunawa, bangare na 22 na sashe 236 na kundin dokar aikata manyan laifuka na 1990, Gwamnatin Tarayya ta halasta wasu nau’uka na yin caca, musamman domin ta samar da kanta, kudaden shiga.
Dokar ta fayyace tsakanin wasan kwarewa wanda yake an halasta da kuma wani wasan, na neman sa a, wanda aka haramta.
Wasu nau’ukan na cacar da aka halasta, sun hada da, cacar da ake sayen wani Tikiti domin shiga gasar zamowa Zakara kan wani abu da aka sanya kamar mota ko wani gida da sauransu.
Amma abin takaici, hakan ya sanya cacar ta kara karbuwa ga wasu alummar gari, musamman a tsakanin yaran da suke da kanannan shekaru.
Kazalika, mun fi lura da akasarin nau’ukan cacar da ake yi a kasar, misali wacce a yanzu ake yi kasar kamar ta gasar ta Kwallon Kafa da sauransu, da ake yi, a kafar Internet.
An yi hasashen cewa, rashin aikin yi, sun arzirta a dare daya, matsain tattalin arziki, su ne, kusan hummulhaba’isin da ke sanya wasu mutanen kasar, musamman matasa ke rungumar wannan halin, inda kuma hakan, ke kara haddasa, aikata manyan laifuka.
Muna damu makuka kan yadda wannan halin, ke kara tarwatsa, tarbiyar wasu matasan kasar, da suka rungimi wannan dabi’ar.
A saboda haka, akwai bukatar Gwamnatin Tarayya, ta dauki matakin kan wannan batun.
Fanin cacar gasar wasa ta Nijeriya, ta kasance a kan gaba a Afirka, duba da yadda a kasuwar a 2023 aka samu ribar da kai ta akalla dala biliyan biyu,
Kazalika, duba da yadda a fannin ake samun sama da tiriliyan uku ko kuma sama da haka, cacar gasar wasa ta Nijeriya, sama da shekarun da suka wuce, wannan fannin, sai kara tumbatsa yake yi kasar, wanda haka na faruwa ne, saboda matsin tattalin arziki, karuwar matasa marasa aikin yi da kuma kara bunkasar yin amfani da wayoyin tafi da gidanka.
Ana dai kara ci gaba da samun irin wadannan shagunan da ake gudanar da irin wannan cacar ta gasar wasanni kusan ako wanne tituna da kuma a dandalin sada zumunta, wanda hakan, ya bai matasan kasar da damar, rungumar dabi’ar ta caca, musamman domin su samar wa kansu, da kudaden shiga,
Zamu iya cewa, mun jahilaci cewa, kasancewar yanayin matsalin tattalin arziki da Nijeriya ke fuskanta ne, ya hadda samun karin guraren da ake gudanar da gasar ta cacar wasanni.
A cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS, samun karuwar matasa marasa aikin yi a kasar, ya sanya su daukar matakan da suke ganin ya dace da su, domin su samarwa da rayuwarsu mafita, musamman yadda suke kara rungumar cacar ta gasar wasanni, da suke mata kallon mataki na zuba hannun jari.
An kiyasata cewa, a wannan fannin, ana samaun akalla Naira tiriliyan uku a shekara, wanda kuma ake kara samun ‘yan kasuwa na tallata hajojinsu ta hanyar amfani da kafar sada zumunta, daukar nauyin tallace-tallacen, da suka samu amincewar wasu fitattu.
Wannan ya nuna yadda rahoton Mujallar Lancet ya bayyana matasan da suka rumgumi cacar ke shafe sa’oi 24 suna gudanar da cacar, wadda kuma ke shafar lafiyarsu da barnatar da kudaden da suke yi.
A bangaren mu, tsawon lokacin da ake ci gaba da fuskanta na kangin matsin tattalin arziki a kasar wanda hakan, ya tilatsa wasu matasan yin cacar ta wasanni, abin damuwa ne.
Bugu da kari, yadda wannan batun ke shafar tabin hankalin matasa da ke yin dabi’ar abin damuwa ne, musamman ganin yadda kwararru a fannin kiwon lafiyar ‘yan Adam suka yi gargadin cewar kara samun matasa masu yin dabi’ar a kasar, na kara jefa matasan a cikin matukar damuwa, inda har wasu matasan saboda fusatar rashin samun nasara a dabi’ar, suke kashe kansu ko kuma rungumar tu’ammali, da kayan maye.
Mai makon su rinka zuba kudaden su a halastattun sana’oi, amma sai buge za zuba kuaden, a cacsar gasar wasannin
Duk da ikirarin da irin wadannan kamfanonin na cacar gasar wanni ke yi cewa, suna samar da nishadi da damar samar da ayyukan yi ga matasan ne, ammu mu dai, mun yi ammanar cewa, suna dai kawai amshe ‘yan kudaden matasan ne.
Babu wata tamtama, akwai bukatar a kakabawa fannin da irin wadannan kamfaonin na cacar gasar wasannin, tsauraran matakai.
Kazalika, akwai matukar bukatar Hukumar sa ido kan irin caca ta kasa NLRC wacce kuma ke sa ido kan cacar gasar wasanni ta kara karfafa dokokin yin gasar cacar ta wasanni tare da daukar matakan da suka kamata, ciki har da sanya dokar tallace-tallace da iyakance yawan kudaden da ake zubawa a cikin cacar, kamar dai, yadda ake yi wasu kasashen duniya.
Hakazalika, ya zama wajibi, Gwamnatocin Jihohi su tashi tsaye, wajen samar da tsare-tsaren da matakai da za su hana matasa shiga cikin dabi’ar.
Idan har mahukunta a kasar ba su samar da daukin da ya dace ba, yunkurin matasan na son arzircewa a dare daya, za ta ci gaba da kasancewa, wanda hakan kuma, zai shafi makoyar matasan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp