Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana matakin da majalisar dokokin kasa ta dauka na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari kwanan nan a matsayin wani lamari mai matukar takaici.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust a ranar Talata.
‘Yan tsirarun ‘yan majalisar sun yi wata ganawa da manema labarai a zauren majalisar kafin su tafi hutun watanni biyu, sun yi barazanar fara shirin tsige Shugaba Buhari a karshen wa’adin makonni shida da suka gindaya, idan shugaba Buhari ya gaza magance matsalolin tsaron kasar nan.
Da yake mayar da martani kan batun, shugaban jam’iyyar APC ya ce matakin wani abin takaici ne wanda bai kamata ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp