Game da kalaman kasar Amurka da suka jibanci hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Talata cewa, abun da Amurka ta fada, ba shi da muhimmanci, maimakon hakan ra’ayin ‘yan Afirka kan hadin-gwiwarsu da kasar Sin shi ne mafi ma’ana.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, wanda ke ziyara a Afirka ta Kudu a jiya Litinin, ya bayyana cewa, kasarsa ba ta da nufin baiwa bangarori daban-daban zabi tsakanin Amurka da Sin, kuma abun da Amurka take fata shi ne, a samar da wani zabi na ainihi.
Har wa yau, fadar White House dake Amurka ta fitar da takardar manyan tsare-tsarenta kan yankunan dake kudu da hamadar Sahara, inda ta ce, kasar Sin na mayar da nahiyar Afirka a matsayin muhimmin dandali, wajen neman cimma muradun kasuwanci da siyasa, da rage alakokin Amurka da jama’a, gami da gwamnatocin kasashen Afirka.
Wang Wenbin ya ce, an cimma dimbin nasarori wajen gudanar da hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka, al’amarin da ya zama sanin kowa, kana, babu wanda ya cancanta ya bata sunan hadin-gwiwar bangarorin biyu.
Ya ce kasashen Afirka ba sa bukatar aminiya wadda za ta rika jirkita gaskiya. Hanyoyin jirgin kasa, da titunan mota, da tashoshin jiragen ruwa, da manyan gine-ginen da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa a Afirka, duk suna nan a zahiri, kuma idanun ‘yan Afirka a bude suke.
Wang ya ce, in dai da gaske Amurka tana son taimakawa nahiyar Afirka, ya dace ta dauki matakan zahiri, maimakon ta yi amfani da manyan tsare-tsarenta kan nahiyar Afirka, don hana ci gaban hadin-gwiwar Afirka da sauran wasu kasashe. (Murtala Zhang)