ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yunkurin Yin Katsa Landan Ba Zai Dakile Ci Gaban Yankin HK Ba

by CGTN Hausa
2 years ago
HK

Kamar dai yadda aka yi tsammani, bayan majalissar dokokin HK ta zartas da kudurin dokar tsaron kasa da gagarumin rinjaye a baya bayan nan, ta kuma cimma nasarar kammala sashe na 23, na dokar gudanarwar yankin na musamman na Sin a ranar 19 ga watan nan, wasu sassa daga kasashen yamma sun zabura, wajen fara sukar wannan mataki, suna masu cewa hanya ce ta dakushe ‘yancin bil adama, kana wasu sun rika nuna shakku, game da yanayin da yankin na HK zai shiga ta fuskar hada hadar kasuwanci.

Amma abun tambaya a nan shi ne, shin wajibi ne a samar da wannan doka ta tsaro? Kuma mene ne ma’anarta ga yankin HK? Alal hakika, zarge-zarge, da kazafi da wadancan sassa suka yiwa Sin ba su da tushe ko makama. Kawai dai akwai wasu mutane a kasashen yamma, dake gudanar da wasan kwaikwayon siyasa da suka saba.

  • Yadda Dimokaradiyya Ke Aiki A Kasar Sin
  • Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2

Ya zuwa yau, mutane sun kara fahimtar wajibcin wannan doka ta tsaron kasa, la’akari da yamutsin da yankin HK ya sha fama da shi mai nasaba da yunkurin “samun ‘yancin kai”, da tashin hankalin da ya biyo bayan hakan, yayin gyaran dokokin jagorancin yankin.

ADVERTISEMENT

A shekarar 2020 ne aka tsara dokar tsaron kasa ta yankin HK, aka kuma aiwatar da ita, wadda ta zama ginshikin samun wadata da daidaito a yankin. Yanzu haka shekaru 3 sun shude bayan wannan ci gaba, kuma tuni yankin HK ya sauya daga wurin da ya sha fama da tashe tashen hankula, zuwa wuri mai cikakken tsarin jagoranci da walwala. To sai dai kuma a daya hannun, kalubalen tsaron kasa da yankin ke fuskanta har yanzu yana da sarkakiya da tsanani.

Wannan doka ta tsaron kasa ta HK, da sauran dokokin da ake aiwatarwa a yankin na musamman na Sin, ba su kai ga wadatarwa wajen shawo kan dukkanin dabi’u, da ayyuka dake iya haifar da barazana ga tsaron kasa ba. Zartas da wannan doka ta yankin HK a wannan karo, na da nasaba da aiwatar da kudurorin tsaron kasa na HK, da cike gibin manufar tabbatar da tsaro a HK, da tabbatar da wanzuwar daidaito na dogon lokaci a HK, da ma cimma nasarar gudanar da manufar nan ta “kasa daya tsarin mulki biyu” bisa daidaito.  (Mai fassara: Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

November 17, 2025
Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin

November 17, 2025
Next Post
amurka

“Taron Koli Na Demokuradiyya” Da Amurka Ke Gudanarwa Na Cike Da Manufunci Da Girman Kai

LABARAI MASU NASABA

NBS

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%

November 17, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

November 17, 2025
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

November 17, 2025
Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

November 17, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin

An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin

November 17, 2025

MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi

November 17, 2025
Tinubu

Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai 

November 17, 2025
Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan

Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan

November 17, 2025
Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

November 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.