• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yunwa Ba Dimokuradiya Ba Ce

by CMG Hausa
3 years ago
Yunwa

Kamfanin watsa labarai na BBC, ya watsa wani labari a kwanan nan, wanda ke cewa jama’ar kasashen Larabawa, suna yanke kauna ga tsarin dimokuradiya irin na kasashen yamma. A ganinsu, tsarin ya hana gwamnati taka rawa yadda ake bukata, a fannonin tabbatar da tsaro da raya tattalin arizki.

BBC ya watsa labarin ne, bisa rahoton da kungiyar binciken ra’ayin jama’a ta Arab Barometer ta gabatar, wanda Michael Robbins, shehun malami na jami’ar Princeton ta kasar Amurka, ya wallafa.

  • Sin Ta Dade Tana Taimakawa Afirka Wajen Samun Ci Gaba Mai Dorewa

Shi kuma wannan malami ya rubuta dalilin da ya sa Larabawa suke yanke kauna ga tsarin dimokuradiya na kasashen yamma, wanda shi ne “mutane na fama da yunwa, suna bukatar burodi.”
Cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, an yi jerin juyin juya hali na daukar tsarin dimokuradiya a wasu kasashen Larabawa.

Zuwa yanzu, ko an samu ci gaban harkoki a wadannan kasashe? Amsa ita ce A’a, ba a samu ba!
Idan mun dauki Tunisia, da Lebanon, da Iraki a matsayin misali, a duk wadannan kasashe, an samu sabuwar gwamnati ta hanyar jefa kuri’a, kuma dukkansu sun dauki tsarin dimokuradiya irin na kasashen yamma. Amma zuwa yanzu, jimillar GDP kan kowane mutum a kasar Tunisia ta yi kasa, idan an kwatanta da na shekarar 2011.

Kana kasar Lebanon ma na fuskantar hadarin rushewar tsarin hada-hadar kudi, yayin da kasar Iraki ke fama da matsalar rashin kwanciyar hankali. Duk wadannan abubuwa sun nuna cewa, tsarin dimokuradiya na kasashen yamma, ba wani abu ne dake iya daidaita dukkan matsalolin da ake fuskanta ba.

LABARAI MASU NASABA

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

Ban da kasashen Larabawa, ko a kasashen yamma, jama’a suna da cikakken imani game da tsarin dimokuradiya irin nasu? Ko alama! Tsohon dan majalisar dattawan Amurka Tom Daschle, ya rubuta wani bayani a kwanan baya, wanda aka wallafa shi a shafin yanar gizo na majalissun kasar Amurka, inda a ciki yake cewa, tsarin dimokiradiya na kasar Amurka “yana daf da halaka kan sa”, sakamakon wasu manyan matsaloli da suka shafi zaman rayuwar jama’a, irinsu bambancin launin fata, da kisan gillar da ake yi da bindiga, da rashin daidaito a fannin samun kudin shiga, da hauhawar farashin kaya, da annobar COVID-19, da dai sauransu.

Hakika duk wata kasa na da irin nata al’adu, da yanayin kasa, wadanda suka sha bamban da juna. Saboda haka, da wuya a ce akwai wani tsarin siyasa mafi kyau, wanda ya dace da kowa. Da ma dai an gabatar da akidar Dimokuradiya, don tabbatar da cewa gwamnati za ta yi kokarin kare hakkin jama’a ne, da biyan bukatunsu.

Idan ko burodi ma ba ta iya samar musu, ko rayuwa ta zama mai wuya a gare su, ke nan wannan “tsarin dimokuradiya” ba na gaske ba ne. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

November 5, 2025
CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika
Daga Birnin Sin

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

November 5, 2025
Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025
Next Post
Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2)

Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2)

LABARAI MASU NASABA

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

November 5, 2025
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025
An Nemi Kasashen ECOWAS Su Samar Da Kariya Ga Yankunan Hakar Ma’adanai

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Sanata Barau Ya Tsaya Takarar Shugaban Majalisar Dattawa

Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio

November 5, 2025
CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

November 5, 2025
Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025
Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.