Ministan harkokin wajen tarayyar Nijeriya Mr. Yusuf MaitamaTuggar wanda ke halartar taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka (FOCAC) na shekarar 2024 a birnin Beijing, ya bayyana cewa, Nijeriya ta dauki wannan kasaitaccen taro da matukar muhimmanci, kuma kasashen biyu sun bayar da sanarwar hadin gwiwa tare da rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama, tuni hadin gwiwarsu ya haifar da da mai ido a fannoni da dama.
Ya ce, “A gaban shugabannin kasashen, an rattaba hannu a kan yarjejeniyoi misali kamar guda takwas, wadanda suka shafi wannan tsari na Belt and Road Initiative (shawarar ziri daya da hanya daya), na yin titi da layukan dogo da wutar lantarki da yanar gizo da yada labarai da kuma musayar labaran ma, abin ya yi kyau kwarai da gaske.”
Mr. Yusuf ya ce, a cikin shekaru da dama da suka wuce, karkashin tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da ma sauran tsarukan hadin gwiwa, kasar Sin ta yi ta inganta hadin gwiwa da Nijeriya ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, matakin da ya haifar da alfanu ga al’ummar Nijeriya. Ya ce, “Ita kasar Sin za ta kara yawan kayayyakin da take shigowa da su daga Nijeriya, ban da na amfanin gona, har ma wanda aka riga aka sarrafa su, inda a cikin sarrafawa, ma’ana ‘yan Nijeriya sun samu aikin yi, kuma su ma sun more wani abu a ciki.”
A game da makomar huldar da ke tsakanin kasashen biyu, Mr.Yusuf ya ce, Sassan biyu za su ci gaba da inganta huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, kuma huldar kasashen biyu na da makoma mai haske. Ya ce, “Mun kuma amince da junanmu cewa, za mu kara karfafa dankon zumunci da ke tsakanin Nijeriya da kasar Sin, sabo da haka da tsarin da muke da shi na tafiya tare, ana ce masa strategic partnership (abokantaka bisa manyan tsare-tsare), yanzu ya zama comprehensive strategic partnership (abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni), wato za a duba bangarori daban daban na kawo ci gaba na shekaru dama.”