Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce yankin Arewa zai ƙara mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen shekarar 2027.
Gwamnan ya faɗi haka ne a wani taro da ake gudanarwa a Kaduna, wanda ke duba yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da harkokin yankin Arewa, musamman a fannoni kamar na tsaro, noma, wutar lantarki da kuma ababen more rayuwa.
- Sin Da Benin Da Thailand Za Su Aiwatar Da Matakan Saukaka Tantance Kaya Na Kwastam
- NiMet Ta Yi Hasashen Samun Mamakon Ruwan Sama A Sassan Nijeriya Cikin Kwana 3
Ya ce goyon bayan da aka bai wa Tinubu a 2023 ya fara haifar da sakamako mai kyau.
A cewarsa an fara ganin canje-canje a ayyukan raya ƙasa.
Taron wanda gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya, ya samu halartar manyan mutane daga Arewa, ciki har da gwamnan Kaduna Uba Sani, da sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume.
Sauran sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci da hafsoshin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp