Jam’iyyar ADC reshen jihar Kaduna ta kaddamar da kwamitin sake fasalin jamiyyar domin ƙarfafa tsarin jam’iyyar a faɗin jihar.
Jam’iyyar ta umarci kwamitin da ya gabatar da rahoton ayyukansa ga sakatariyar jihar cikin kwanaki 14.
- Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi
Mambobin kwamitin sun haɗa da: Hon. Philimon Kure daga shiyya ta 3 wanda zai kasance Shugaban kwamitin sai Honorable Muktar Isa Hazo ( na jamiyyar SDP daga shiyya ta daya sai Muhammed Dauda Haskiya na jam’iyyar SDP daga shiyya ta daya da Honorable Kabiru Ajuji daga jam’iyyar APC daga shiyya ta daya da Zulaihat Abdul Kareem daga ADC Mataimakiyar Shugaba a shiyya ta daya .
Sauran sun haɗa da: Hon. Ibrahim Adamu Sarki a jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu sai , Nazifi Jibrin Muhammad na jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu da Haruna Dogo Mabo na.jamiyya NNPP daga shiyya biyu sai Honorable Isah Dan Maryam na PRP daga shiyya ta biyu da , Honarabul Isaac Auta Zankai na jam’iyyar SDP da Wilson Iliya Yange na jam’iyyar PDP, da Honarabul Simon Na Allah na jam’iyyar LP, sai Ibrahim Musa na jam’iyyar ADC daga shiyya ta biyu shi ne Sakataren kwamitin.
Da yake jawabi bayan kaddamar da kwamitin, Shugaban jam’iyyar na jihar, Elder Patrick Ambut, ya shawarci mambobin da su kasance masu jajircewa tare da tabbatar da adalci da gaskiya a cikin aikin da aka dora musu.
“Kalubalen aikin yana da girma kuma yana buƙatar jajircewa, adalci, da gaskiya,” in ji shugaban jam’iyyar”
Daga cikin ayyukan da aka ɗora wa kwamitin har da: yin binciken shugabanci a dukkan ƙananan hukumomi 23 da mazabu, tare da daidaita tsarin jam’iyyar da baban taron jam’iyyar na 2022 da hukumar INEC ta kula da shi.
A cikin jawabinsa na karɓar nauyin shugabanci, Shugaban Kwamitin, Philimon Kure, ya bayyana cewa ayyukan da aka ɗora musu sun bayyana sosai, yana mai cewa gudunmawar kowa da kowa ce za ta tabbatar da gina jam’iyya mai ƙarfi wacce za ta kare muradun dukkan mambobi.













