Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana dan takarar jam’iyyar NNPP, Alhassan Ishaq, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Kura/Garun Mallam a jihar Kano.
Jami’in zabe na INEC Farfesa Shehu Galadanchi ne ya bayyana cewa Ishaq na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 37,262 inda ya doke Musa Daurawa na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 30,803.
- INEC Ta Dakatar Da Sake Zabe A Kano, Enugu, Akwa Ibom Sakamakon Ayyukan ‘Yan Daba
- INEC Ta Shirya Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihar Kano
Idan dai za a iya tunawa kotun daukaka kara ta umarci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfuna 20 na mazabar Kura/Garun Malam a jihar Kano.
Haka kuma, INEC ta ayyana Bello Butu-Butu na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Rimin Gado/Tofa.
Jami’in zabe na zaben Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ne ya sanar da Bello Butu-Butu na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 31,135 inda ya doke abokin takararsa na APC wanda ya samu kuri’u 25,577.
A baya Kotun daukaka kara ta umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 33 a mazabar jihar Rimin Gado/Tofa.