Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Mahmoud Musa Kallamu, a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbin a mazabar karamar hukumar Mayo-Belwa.
Da yake sanar da sakamakon zaben, jami’i mai sanar da sakamakon, Farfesa Muhammed Baba Ardo, ya ce, dan takarar jam’iyyar PDP, Musa Kallamu, ya lashe zaben da kuri’u 1306, inda yayi nasara akan dan takarar jam’iyyar APC, Ibrahim Musa Italiya, da ya samu kuri’u 874.
- Zaɓen Cike-gurbi: PDP Ta Yi Nasarar Lashe Zaɓen Kujerar Majalisar Tarayya A Jihar Jigawa
- Hukuncin Zaben Adamawa: Na Rungumi Kaddara – Binani
Jami’in hukumar zabe ta INEC, Farfesa Muhammad Ardo, ya ce, Musa Kallamu na jam’iyyar PDP ya lashe zabe a rumfuna shida daga cikin bakwai da hukumar ta gudanar da zaben cike gurbin.
Ya ci gaba da cewa “Mahmoud Musa Kallamu na PDP, bayan ya cika sharuddan doka, an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbin a karamar hukumar Mayo-Belwa” inji Farfesa Ardo.
Farfesa Muhammed Ardo ya ce cikin jimlar kuri’u 5024 da aka yiwa rajista a zaben, kuri’u 2252 da aka amince dasu, 2192 masu inganci, kuri’u 06 ba’a amincewa dasu ba, yayin da kuri’u 2252 aka kada lokacin gudanar da zaben.
Da yake magana bayan sanar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben Musa Mahmud Kallamu, ya yabawa jama’ar mazabarsa bisa goyon baya da suka nuna masa, ya kuma ba su tabbacin ba zai ba marada kunya ba.