Connect with us

LABARAI

Za A Binciki Dukkan Masu Laifin Cin Hanci Da Rashawa – Buhari

Published

on

A jiya Juma’a Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin zai warware dukkan matsalolin rashawa a Nijeriya.
Shugaba Buhari ya ce, duk wasu shari’o’in cin hanci da rashawa da suka gabata da na yanzu za a sake bincikarsu.
Shugaban kasar ya bayya hakan ne hakan ne a Fadarda da ke Abuja, wannan bayanin kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu.
Haka kuma shugaba Buhari ya koka da yadda cin amana da rashawa suka zama rowan dare a gwamnatocin baya.Ya yi bayanin cewa, za a kafa kwamitin bincike wanda zai gano masu irin wadannan laifuka.
Haka kuma ya ce “Za a bincika dukkan shari’ar da ta gabata da ta yanzu.
“Dukkan wasu kararraki za a gano su kuma hukumarsu za ta yi aiki da su sosai.
“Wannan ne ya sa muka kafa hukumar bincike da wuri.
Advertisement

labarai