Iyalan marigayi Alhaji Aminu Dantata sun tabbatar da cewa za a binne shi a birnin Madina, Saudi Arabia, kamar yadda ya ba da wasiyya kafin rasuwarsa a ranar Juma’a da ta gabata a Dubai.
Majiyoyi daga cikin iyalan sun bayyana cewa marigayin ya ba da umarnin a binne shi kusa da gidan da ya mallaka a Madina.
Jana’izar Kano:
– Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta shirya Sallar ga’ibi (mamaci)
– Za a yi salla a Masallacin Umar Bin Khattab, shataletalen Dangi, Kano
– Lokacin: Asabar 2:00 na rana.