A jiya ne, aka yi taron manema labarai game da bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2023 wato CIFTIS a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Za a gudanar da bikin baje kolin cinikayyar hidima na shekarar 2023 mai taken “Bude kofa yana haifar da ci gaba, hadin gwiwa da samun nasara a nan gaba” a cibiyar taron kasa da kasa ta kasar Sin da yankin Shougang dake yammacin birnin Beijing daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Satumba.
Kasashe da yankuna guda 27 za su kafa rumfunan nune-nune a bikin, ciki har da kasar Georgia da kasar Sudan da kuma Asusun tallafawa yara na MDD wato UNICEF, wadanda a karo na farko za su halarci bikin. Kuma babbar bakuwa a wannan karo, kasar Burtaniya za ta tura tawagar wakilai zuwa bikin, wadda za ta kasance mafi girma cikin tarihin shirya bikin.
Haka kuma, a biki na wannan karo, za a mai da hankali kan harkokin dake shafar kasashen duniya, da kara bude kofa domin zurfafa hadin gwiwar tsakanin kungiyoyin kasashen duniya, da gudanar da taron kolin cinikayyar hidima na duniya. Kana, kungiyoyin kasa da kasa irinsu kungiyar raya harkokin masana’antu ta MDD wato UNIDO, da kungiyar kare ikon mallakar fasaha ta duniya wato WIPO, da hukumar hasashen yanayi ta duniya wato WMO za su gudanar da nune-nune a yayin bikin na CIFTIS. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)