Daga ranar 29 ga watan Yuni zuwa ranar 2 ga watan Yuli mai zuwa, za a gudanar da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na 3 a birnin Changsha dake lardin Hunan na kasar Sin.
Ya zuwa yanzu, akwai kasashen Afirka guda 53, da kungiyoyin kasa da kasa guda 8, da larduna da yankuna da biranen kasar Sin guda 30, da kuma kamfanoni mallakar gwamnatin Sin, kungiyoyin kasuwanci, da hukumomin sha’anin kudi sama da 1500, sun yi rajistar halartar wannan muhimmin biki.
Kasashen Afirka guda 8 da za su hada da kasashen Benin, da Congo (Kinshasa), da Madagascar, da Malawi, da Morocco, da Mozambique, da Najeriya, da Zimbiya, za su zama manyan bakin gudanarwar bikin, kuma, lardin Shandong da lardin Hubei na kasar Sin za su jagoranci bikin.
Bisa labarin da aka fidda, akwai kamfanoni sama da 1350 za su halarci bikin na wannan karo, adadin da ya karu da kashi 55 bisa dari idan aka kwatanta da na biki na gaba. Kana, bisa hasashen da aka yi, yawan ’yan kasuwa da masu kallo zai kai dubu 8, kana, mutane sama da dubu 100 za su ziyarci bikin.
Ban da haka kuma, za a gudanar da bikin nune-nunen sakamakon da aka samu bisa hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin aiwatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da kuma fannin yadda ’yan matan Sin da Afirka suke yin kirkire-kirkire.
Bugu da kari, kasashen Afirka guda 8 da za su kasance manyan baki na bikin, za su kafa dandalin nune-nune na kansu, domin nuna kayayyaki da al’adunsu na musamman. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)