Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta bayyana a yayin taron manema labarai da aka shirya Alhamis din nan cewa, bayan ingantawa da daidaita manufofin rigakafin cutar a kasar Sin, kamfanonin kasar Sin da na kasashen waje sun riga sun cika sharuddan shiga baje kolin a zahiri. Tun daga wannan baje kolin kasuwanci na bazara, baje kolin na Canton zai ci gaba a zahiri daga dukkan fannoni. An shirya gudanar da bikin baje kolin na Canton karo na 133 a birnin Guangzhou a matakai uku daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa 5 ga watan Mayu.
Kasar Netherlands ta ce za ta takaita fitar da fasahar sassan laturoni. Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta bayyana fatan cewa, kasar Netherland za ta ci gaba da cimma burinta na dogon lokaci da kuma ka’idojin kasuwa mai adalci da daidaito, da kiyaye ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, ba tare da cin zarafin matakan hana fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare ba. (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp