Yau Litinin, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya amsa tambayoyin ‘yan jarida game da matakin kasar Amurka, na fara sabon zagayen sayar da makamai ga yankin Taiwan.
Wu Qian ya ce, Amurka ta sayar wa yankin Taiwan na Sin makamai, wanda hakan ya keta manufar kasar Sin daya tak, da kuma kudurorin dake kunshe cikin takardu uku da Sin da Amurka suka amincewa, kuma ya keta ikon mulkin kasar Sin da moriyar tsaronta, ya gurgunta dangantakar ayyukan sojin kasashen biyu. Kaza lika, matakin ya gurgunta zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan.
- An Kama Wani Dan Jihar Nasarawa Da Damfarar Masu Neman Aiki
- Gwarzon Gwamna Na Shekarar 2024: Fasto Umo Bassey Eno
Bangaren Sin ya bukaci Amurka da ta cika alkawuran da ta dauka, cewa ba za ta goyi bayan “Yancin kan Taiwan” ba, ta kuma daina baiwa Taiwan makamai ta kowace hanya, da daukar matakai na zahiri, don kiyaye dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da sojojin kasashen biyu.
Rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin za ta ci gaba da karfafa horar da sojoji, da shirye-shiryen yaki, da kuma dakile duk wani yunkurin ballewa, na neman “Yancin kan Taiwan”, da tsoma baki daga kasashen waje. (Safiyah Ma)