Dame (Dr.) Adaora Umeoji, ita ce manajan darakta kuma shugabar Bankin Zenith Plc, tun daga watan Yunin 2024 har zuwa yanzu, ta samu wannan lambar yabon ta Leadership saboda kyakkyawan jagoranci da ƙwarewa da kuma sadaukarwarta wajen tabbatar ingantaccen tsarin tafiyar da harkokin banki.
Wasu daga cikin ɓangarorin da ta yi gagarumar nasara a kai, sun haɗa da kafa tarihin samar da riba a ƙarƙashin jagorancinta, inda Bankin Zenith, ya samu naira tiriliyan ɗaya cikin watanni tara na farkon shekarar 2024, samun ƙaruwar kashi 98.57% hakan ke nuna samun ƙarin riba kan yadda aka saba samu a duk shekara, a ɗayan bangaren kuma babbar ribar bankin ta kai Naira tiriliyan 2.8, yadda hakan ke nuna samun ƙaruwar kashi 118.16%.
- Karancin Kudin Shiga Ya Jefa ‘Yan Nijeriya Miliyan 14 Cikin Kangin Talauci – Bankin Duniya
- Katafaren Aikin Karkatar Da Ruwa Na Sin Ya Karkata Kyubik Mita Biliyan 76.5 Zuwa Arewacin Kasar
Umeoji, ta yi nasarar zamanantar da tsarin harkokin bankin tare da faɗaɗa damar hada-hadar kuɗaɗe ta fuskar amfani da kididdigar jama’a don fahimtar abin da kowanne rukuni na jama’a ke buƙata, wannan mataki ya ƙara wa Bankin Zenith karɓuwa a matsayin jagora kuma abin amincewa ga masana’antu a harkokinsu.
Ta yi amfani da ƙwarewa a jagoranci da hangen nesa ta hanyar amfani da gogewar da take da ita na sama da shekaru 30 a aikin banki, ciki har da shafe shekaru 26 da ta yi a Bankin Zenith, inda ta samar da ci gaba wajen kyautata tsarin aiki da kawo sababbin dabaru don inganta hulɗa da abokon kasuwanci da janyo hankalin sauran jama’a ga bankin.
Tarin Ilimi da ficen da shugabar ta yi a ɓangarori daban-daban wajen samun shaidun karatu da dama da suka haɗa da digirin digirgir kan gudanar da kasuwanci daga Jami’ar Harvard na Columbia da makarantar MIT, ta kuma kasance ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar ƙwararrun ma’aikatan bankuna na Ingila, sai kuma manyan shaidun karramawa da ta samu a Nijeriya, da kuma ta babbar hadima a majami’ar St. Sylvester.
Umeoji, ta kasance mace mai ɗa’a da martaba ɗabi’un aikin banki musamman a matsayinta na wadda ta kafa ƙungiyar mabiya Katolika na Ma’aikatan Banki ta Nijeriya (CBAN), inda take bayar da shawarwari kan harkokin banki da cinikayya ta yadda al’umma za su amfana daga tarin iliminta da ƙwarewarta.
A.taƙaice dai, ko shakka babu jagorancin Umeoji, yana nuni da irin tsayuwar dakar da take wajen ƙirƙire-ƙirƙire da fito da sababbin dabaru da kuma mayar da hankali wajen sanya harkar banki ta kasance mai tasiri, musamman a bangaren hada-hadar kuɗi na ƙasarnan.