Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a ci gaba da gudanar da zaman makokin marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a babban birnin tarayya, Abuja.
Mai magana da yawun marigayin, Malam Garba Shehu, ya ce daga ranar Laraba ne mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, tare da ministoci 22 da ke tare da shi za su kammala zaman makoki a Daura, Jihar Katsina.
- Atiku Abubakar Ya Fice Daga PDP, Duba Dalili
- Xi Jinping Ya Mika Sakon Ta’aziyya Zuwa Ga Takwaransa Na Najeriya Bisa Rasuwar Muhammadu Buhari
Ya ce daga nan za su koma Abuja don ci gaba da taron addu’a da karɓar gaisuwar rasuwa daga jama’a da manyan jami’an gwamnati, ciki har da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da shugabannin majalisar dokoki da na shari’a.
Garba Shehu, ya kuma bayyana cewa gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, zai ci gaba da karɓar gaisuwar jama’a a gidan gwamnati da ke Katsina.
Hakazalika, uwargidan marigayin, Hajiya Aisha Buhari, da ’ya’yansu za su koma Kaduna a ranar Juma’a, inda za su ci gaba da karɓar gaisuwar mutane daga sassa daban-daban na ƙasa.
A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da addu’o’i a masallatai a faɗin ƙasar don roƙon Allah Ya gafarta wa marigayin.
An ci gaba da bayyana Buhari a matsayin shugaba mai gaskiya da jajircewa, wanda ya yi ƙoƙari wajen ganin Nijeriya ta samu zaman lafiya da ci gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp