Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), ta ce za a gudanar da kidayar jama’a a fadin kasar nan na shekarar 2023 daga ranar 29 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu.
Shugaban NPC, Nasir Kwarra ne, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Dimokuradiyya Ta Zauna Daram A Nijeriya, Ba Batun Juyin Mulki – Shugaban Tsaro
- Yadda Za Ka Sauke Bidiyo A Wayarka Daga Facebook Da YouTube
Shugaban NPC ya ce “A ranar 29 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, ma’aikatanmu za su kasance a fagen daga don kidayar mutane.”
Kwarra ya yi alkawarin cewar aikin zai sha bamban da na baya domin za a gudanar da shi ne da fasahar zamani.
Da yake tabbatar da hakan, shugaban NPC, ya jaddada cewa kidayar za ta kasance mafi inganci.
Saboda haka, ya bayyana cewa hukumar za ta yi amfani da hotunan tauraron dan adam da GPS kuma za ta sanya lambar kowane gini da ke kasar nan cikin kidayar.
Shugaban NPC ya bayyana hukumar ta kammala daukar ma’aikatan da za su yi aiki tare da ita a dukkanin kananan hukumomi 774.
Idan ba a manta ba rabon da a yi kidayar mutane tun shekarar 2006, lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp