Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da cewa za ta fara ba da sufuri kyauta ga ma’aikatan gwamnati, masu ritaya da ɗalibai daga ranar Litinin, 7 ga Yuli, 2025, a ƙarƙashin shirin Kaduna Subsidised Transport Scheme (KSTS).
Darakta Janar na Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Kaduna (KADSTRA), Inuwa Ibrahim, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce za a ba waɗannan rukuni uku damar amfani da motocin kyauta har na tsawon watanni shida.
- Uwargidan Gwamnan Kaduna Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Noma Ga Mata Manoma
- Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tabbatar Da Kisan Jami’anta A Kaduna Da Neja
Ibrahim ya ƙara da cewa dukkan ɗalibai, ko na makarantar gwamnati ko masu zaman kansu, daga matakin firamare zuwa manyan makarantu, za su amfana da wannan tsari. Ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin kokarin Gwamna Uba Sani na saukaka rayuwa ga ma’aikata, dalibai da tsofaffin da suka yi ritaya daga aiki.6
An bayyana cewa ma’aikatan gwamnati za su sami damar hawa motocin ne ta hanyar nuna katin shaida na aiki tare da lambar NIN domin hana amfani da tsarin ba bisa ƙa’ida ba. Ɗalibai kuwa sai sun kasance cikin cikakken kayan makaranta kafin su hau motar, yayin da jami’an tsaro daga hukumomin da aka amince da su za su iya hawa bayan sun gabatar da shaidarsu ta aiki.
Darakta Janar din ya jaddada cewa za a gudanar da wannan sufuri ne cikin tsari da tsauraran matakan tsaro da bin doka, domin tabbatar da ingantaccen aiki da aminci. Ya buƙaci al’umma su haɗa kai da jami’an sufuri domin cimma nasarar shirin, yana mai cewa motocin farko za su fara zirga-zirga a hanyoyin da aka ware daga ranar Litinin mai zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp