Gwamnmati a Ingila ta tabbatar da cewa za ta haramta kayan cin abinci wadanda ake amfani da su sau daya ana jefarwa, kamar cokali da farantan soso.
Ba a san yaushe ne harmacin zai fara aiki ba, amma hakan na zuwa ne bayan irin wannan yunkuri a yankunan Wales da Scotland.
Sakatariya mai kula da harkar muhalli, Therese Coffey ta ce za a yi hakan ne saboda a kare muhalli domin amfanin al’ummar da za ta zo nan gaba.
Masu hankoro sun yi maraba da shirin, sai dai sun bukaci a bullo da karin hanyoyin rage amfani da robobi.
Alkaluman gwamnati sun nuna cewa ana amfani da kwanukan cin abinci na soso guda biliyan 1.1, da cokula da wukaken robar sama da biliyan hudu a kasar, cikin kowace shekara.
Ba kasafai ba ne sharar robobi takan rube ba, inda take zama a cikin shara tsawon shekaru.
Duk da kwanuka da cokulan soso kan taimaka ta bangaren tsafatar abinci to amma ta kan kare a matsayin shara, inda ta kan lalata kasar noma da rafuka.
Matakin gwamnatin na zuwa ne bayan jerin tattaunawa da masu ruwa da tsaki, kuma za a wallafa matakin ne a watan Janairun da muke ciki.
Alkaluma sun nuna cewa a kasar ta Ingila kowane mutum na amfani da akalla farantin cin abinci na roba guda 18 da kuma cokula da wukaken cin abinci 37 a kowace shekara, inda kashi 10 na irin wadannan robobi ne kawai ake sake sarrafa su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp