• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za A Iya Gamawa Da ‘Yan Bindiga Cikin Mako 2 Idan An Yi Niyyar Haka – Gwamna Dauda

by Leadership Hausa
1 year ago
yan bindiga

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa za a iya magance ‘yan bindiga, waɗanda suka mayar da garkuwa da mutane sana’a, cikin makonni biyu idan aka yi niyyar hakan.

Gwamnan ya koka kan yadda ’yansanda da sojoji suka sanya sakaci a yaƙi da ’yan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma.

Gwamna Lawal bayyana haka ne a wani jawabi kai tsaye da ya gabatar cikin a shirin SUNRISE DAILY na gidan talabijin na CHANNELS TV a ranar Talatar nan.

“A mako biyu za su zama tarihi amma ba a shirya hakan ba a siyasance, mun san su waye ’yan bindigar nan kuma mun san wurin da suke rayuwa,” inji Dauda Lawal.

  • NAF Ta Hallaka ‘Yan Bindiga 29 A Katsina

 

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22

A Ba Mu Makamai Don Kare Kanmu – Jama’ar Sakkwato

Ya ce, irin salon hukumomin tsaron Gwamnatin Tarayya ya sa aka samar da Rundunar Tsaron Jihar masu suna ‘Askarawan Zamfara’.

Gwamna Dauda Lawal ya ce, “Mu a matsayinmu na gwamnoni, ba mu da iko a kan sojoji, ba mu da iko a kan ’yansanda da jami’an tsaron farin kaya, shi ya sa galibi abin ke sa mu cikin damuwa.

“Za ka ga a lokacin da muke buƙatar waɗannan dakarun tsaro, ba za a same su ba, bisa haka ne muka ga mafita kawai mu kafa rundunarmu ta kanmu.”

Gwamna Lawal ya yi zargin cewa wasu abokan hamayyarsa na siyasa suna tattaunawa da ’yan bindiga ba da saninsa ba.

Lokacin da aka tambaye shi ko ya san ainihin waɗanda ke tattaunawa da ‘yan bindigar, sai ya ce, “Duk abin da suke yi mun sani.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
Tsaro

Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22

October 12, 2025
Gwamna Aliyu Ya Tsige Hakimai 15 Na Sokoto
Tsaro

A Ba Mu Makamai Don Kare Kanmu – Jama’ar Sakkwato

October 11, 2025
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno
Tsaro

Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno

October 11, 2025
Next Post
Xi Ya Ba Da Amsa Ga Wasikar Farfesan Jami’ar Tsinghua

Xi Ya Ba Da Amsa Ga Wasikar Farfesan Jami’ar Tsinghua

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

October 17, 2025
Tinubu

Batun Yin Afuwa Ga ‘Yan Yankin Ogoni Huɗu

October 17, 2025
Shettima

‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima 

October 17, 2025
Manzon Allah

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

October 17, 2025
An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai

Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma

October 17, 2025
Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa Da Kamfanin Sin Ya Gudanar A Birnin Abuja

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura

October 17, 2025
Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

October 17, 2025
Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.