Gwamnatin Tarayya ta ce za a kammala aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kano cikin shekara guda.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Sunday Dare, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware kuɗaɗen da za a yi amfani da su don kammala aikin da ya tsaya.
- Hasashe Kan Tarukan CPPCC Da NPC Na 2025
- Boko Haram Sun Sace Farfesan Jami’ar Sojoji Da Ke Jihar Borno
“A ranar Litinin, Shugaba Tinubu ya amince da kasafin kuÉ—in da za a kammala wuraren da ba a gama ba a kan titin Abujazuwa Kaduna da na Kaduna zuwa Zaria cikin wata 12,” in ji shi a shafinsa na X.
A baya, Gwamnatin Tarayya ta dakatar da tsohon kamfanin da ke aikin titin, Julius Berger, saboda tsaikon da aka samu.
A watan Janairu ne aka bai wa wani sabon kamfani aikin don ya ƙarasa titin.
Aikin titin Abuja zuwa Kano dai yana da matuÆ™ar muhimmanci ga tafiye-tafiye da kasuwanci a Arewacin Najeriya, kuma jama’a sun daÉ—e suna Æ™orafi kan jinkirin kammala shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp