Babban mai tsara rokar Long March daya tilo na kasar Sin da ake amfani da ta a aikin harba ‘yan sama jammati, ya bayyana dalilin da ya sa rokar Long March-2F, ta kasance mafi inganci, da tsaro wajen harba ‘yan sama jannatin kasar Sin zuwa sararin samaniya.
Babban mai tsara rokar Long March-2F na cibiyar koyar da fasahar harba kumbuna ta kasar Sin, Rong Yi ya bayyana a wata hira da ya yi da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) cewa, rukunin Long March-2F ya ci gaba da bunkasa yayin da aka fara bunkasa shi daidai da shirin binciken sararin samaniyar kasar Sin.
A matsayinsa na wani nau’in roka daya tilo da kasar Sin ta kera don gudanar da ayyukan harba ‘yan sama jannati, rokar Long March-2F sun yi nasarar harba kumbuna har sau 19, tun bayan da suka fara aikin a shekarar 1999.
Za a yi amfani da rokar wajen kara harba ‘yan sama jannati zuwa tashar sararin samaniyar kasar Sin duk bayan watanni shida, yayin da tashar binciken sararin samaniyar kasar ta kama aiki gadan-gadan a karshen 2022. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)