A ranar Asabar na makon jiya ne Ministan Harkokin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya kafa kwamiti na musamman don kawo karshen haramtattun harajin da ake kakaba wa masu shigo da kaya ta filayen jiragen kasar nan.
Idan za a iya tunawa an bayar da rahoton yadda masu shigo da kayayyaki daga kasashen waje suka nuna damuwarsu a kan yadda ake karbar harajin Dala 35,00 a kan shigo da kaya mai nauyin tan 100 a filayen jiragen Nijeriya yayin da ake karbar Dala 3,000 a kan kaya mai nauyi iri daya a filayen jiragen saman kasa Ghana.
- Maddison Na Tottenham Zai Yi Jinyar Watanni 2 Bayan Ya Samu Rauni A Kafarsa
- Yawan ‘Yan Nijeriya Ya Doshi Miliyan 223 – Shugaban NPC
Sun bayyana cewa, haka na faruwa ne saboda harammattun haraji da wasu hukumomin gwamnati ke karba a hannun masu shigo da kaya da basu da ka’ida.
A kan haka Keyamo ya kafa kwamitin ya kuma nemi kwamitin ta gaggauta gano hukumomin gwamnatin da suke karbar harajin da ba bisa ka’ida ba, ya kuma sanar da ba kwamitin mako biyu don kammala aikinsu.
An tattaro da mambobin kwamitin ne daga bangaren masu harkar jiragen sama, hukumar kula da tashoshin jiiragen sama ‘Federal Airports Authority of Nigeria (FAAN)’ da kuma kungiyar ma’aika masu aiki a filayen jiragen sama ta kasa, ‘National Association of Nigerian Travel Agency (NANTA)’, ‘Ground handlers’ da kuma ma’aikatar harkokin jiragen sama.
Ministan ya kuma nuna damuwarsa a kan yadda kamfanonin jiragen sama na ‘yan kasa suke saurin mutuwa, inda ya yi alkawarin cewa, gwamnatin tarayya za ta samar da hanyoyin tallafa musu, ya ce a cikin shekara 20 zuwa 25 kamfanonin jiragen sama na ‘yan kasa fiye da 100 suka durkushe.