Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron majalisar gudanarwar kungiyar hadin gwiwar Shanghai (SCO) karo na 24 a birnin Astana, da kuma ziyarar aiki a kasar Kazakhstan, za a nuna zango na 3 na shirin bidiyo, mai taken “Labarun da Xi Jinping ya fi kauna” da harshen Kazakhstan, ta kafofin watsa shirye shirye daban daban dake kasar, wanda kafar CMG ta kasar Sin ta tsara, tun daga yau Talata 2 ga watan nan na Yuli.
Shirin bidiyon ya mayar da hankali ne ga nuna yadda ake cimma nasarar bai daya, da kare muhallin halittu, da al’adun gargajiya, da mabanbantan al’adu da sauran muhimman batutuwa, kana zai nunawa masu kallo tushen al’adun kasar Sin na turbar zamanantar da kasa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp