Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta gargadi mazauna wasu jihohin Arewacin kasar nan da su shirya tsaf domin samun ruwan sama mai karfi a cikin kwanaki masu zuwa.
A cewar wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, “A halin yanzu ana ganin tsawa a sassan Arewacin kasar nan da suka hada da Borno, Taraba, Gombe, Bauchi da Kano.
- Buhari Ya Nada Sabon Mai Ba Shi Shawara Kan Sha’anin Tsaro
- Mutum 10 Sun Mutu Bayan Shan Shayin Gadagi A Wajen Daurin Aure A Kano
Ana sa ran wadannan za su yadu zuwa yamma 0don ba da tsawa daidai gwargwado ga wasu biranen.”
Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran samun masu tsawa a halin yanzu wanda za ta yadu zuwa gabas zuwa garuruwan Filato, Abuja, Nasarawa, Jigawa, Adamama, Yobe da Borno,
Jihohin Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano da Katsina su ma za su fuskanci yanayin.
NiMet ta ce a yankunan da ake sa ran tsawa, ana iya samun iska mai karfi kafin damina kuma a saboda haka, ana iya sare itatuwa, da igiyoyin lantarki, da abubuwan da ba a tabbatar da su ba, da kuma raunanan gine-gine, don haka ana shawartar jama’a da su yi taka tsantsan tare da zama a gida musamman a lokacin ruwan sama kamar da bakin kwarya don gudun kada walkiya ya same su.
NiMet ta shawarci dukkan ma’aikatan jirgin sama da su yi amfani da rahotannin yanayi lokaci-lokaci don ingantaccen shiri a ayyukansu.
Ta kara da cewa matsakaicin ruwan sama zai iya haifar da ambaliya.
Haka kuma an bukaci hukumomi da daidaikun jama’a da su tashi tsaye domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi a lokacin damina.