Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Femi Fani-Kayode, ya bayyana fatansa na ganin cewa, nan ba da jimawa ba an kawo karshen kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a Gaza da kuma take hakkin bil adama da Sojojin Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa.
Mista Fani-Kayode, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata a yayin bikin ranar Aqsa na 2024 da kungiyar wayar da kan musulmi ta kasa da kasa ta shirya a Legas, ya danganta fatansa kan yadda duniya ke nuna bacin rai da ya biyo bayan kisan kiyashin.
- Wakilin Kasar Sin Ya Bukaci Amurka Da Ta Matsawa Isra’ila Ta Dakatar Da Ayyukan Soji A Gaza
- Hamas: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Isra’ila Saboda Ƙin Amincewar Ƙasar Kan Tsagaita Buɗe Wuta
A cewar rahotanni, an kashe mutane fiye da 40,000 da suka hada da mata da yara a yakin da ake ci gaba da gwabzawa.
Ya ce: “Wajibi ne a kan mu da duk mutum mai hankali ya yi magana kan wannan barnar ta asarar rayukan al’umma.
“Kuma na yi farin ciki cewa, zanga-zangar adawa da mugun aikin Isra’ila tana faruwa a duk faɗin duniya a yau. Tana faruwa a Amurka. Tana faruwa a Turai. Afirka ta Kudu ce ke kan gaba a nahiyar Afirka, kuma mutane da yawa suna tofa albarkacin bakinsu.
“Ireland ta yi Allah wadai da hakan. Belgium ta yi Allah wadai da hakan. Spain ta yi Allah wadai da hakan. Kashi 90 cikin 100 na kasashen Kudancin Amurka sun yi Allah wadai da hakan. Mutane da dama a cikin Faransa sun yi Allah wadai da hakan. Hatta Birtaniya ta rage sayar wa Isra’ila da makamai.
“Duniya duka tana yin Allah wadai da aikin Isra’ila. Manyan cibiyoyin karatu a Amurka, kamar Harvard, Yale, Oxford, da Cambridge, sun yi zanga-zangar adawa da abin da ke faruwa a Gaza.
“Yadda muke fada, da yadda muke magana kan abin da ke faruwa a Gaza a yau, shi ne irin yadda mutane suka yaki wariyar launin fata a Afirka ta Kudu wanda hakan ya bai wa kasar ‘yanci. Don haka, lokaci ne kadan ya rage al’ummar Falasɗinawa su samu ‘yanci na gaskiya.
“Muna yin furucin adawa da aikin Isra’ila a nan ta hanyar yin magana a kullum a kasarmu Nijeriya. Dan adam, a ko ina yake Dan Adam ne, Babu ruwanmu da banbancin addini.