Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi ta shirya mukabala tsakanin malamai da kuma Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi kan kalaman da ya yi game da Fiyayyen Hallita, Annabi Muhammadu (SAW).
Wata wasika da hukumar ta aike wa malamin, dan asalin Jihar Bauchi, ta ce za a gudanar da tattaunawar ilimin ne ranar Asabar, 8 ga watan Afrilu a jihar.
- Hajjin 2023: Miliyan 3 Kowane Maniyyaci Zai Biya A Bana —NAHCON
- ‘Yan Majalisu Tara Da Ke Zawarcin Kujerar Gbajabiamila
A farkon makon nan ne kalaman malamin suka fara tayar da hazo musamman a kafafen sada zumunta, bayan ya yi ikirarin cewa “ba ya bukatar taimakon Annabi”.
“Ana gayyatarka zuwa tattaunawa ta ilimi game da kalamanka cewa ‘kai! …Manzon Allah ma ba ma son taimakonsa, karewarta ke nan’,” kamar yadda hukumar ta bayyana cikin wasikar.
An ga malamin ya bayyana cikin wani faifan bidiyo a ranar Alhamis yana cewa ya ji daga wata majiya cewa zai yi muhawara da wakilan wasu kungiyoyin Addini a jihar, wadanda suka hada da Izala da darika.
An yi irin wannan muhawara a Jihar Kank a 2021 lokacin da aka zargi Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da yin kalaman batanci ga Annabin Muhammadu.
Bayan muhawarar ne kuma, hukumomi suka gurfanar da malamin a gaban kotu, wadda ta yanke masa hukuncin kisa.