A yau Alhamis ne aka gudanar da taro karo na 4, tsakanin ministocin harkokin wajen kasar Sin da kasashen Tsakiyar Asiya, a birnin Xi’an na lardin Shaanxi. A yayin taron karo na 3 da ya gudana a watan Yunin shekarar 2022, an amince da kafa tsarin taron shugabannin kasar Sin da kasashen Tsakiyar Asiya.
Kaza lika bangarorin da suka halarci taron, sun tattauna don gane da ajandar taron koli da za a gudanar a kasar Sin, da batun hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Tsakiyar Asiya a fannoni daban daban, da al’amuran kasa da kasa, da na shiyyoyi da ke jawo hankulansu duka.
Bayan taron na jiya, ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya sanar da cewa, an tsai da kudurin gudanar da taron koli na kasar Sin da kasashen Tsakiyar Asiya, a wata mai zuwa a birnin na Xi’an.
Har ila yau da yammacin jiyan, ministocin harkokin wajen kasashe 6 da suke halartar taron, sun halarci bikin kaddamar da jirgin kasa na musamman, mai zirga-zirga tsakanin Xi’an da kasashen Tsakiyar Asiya, mai suna Chang’an, inda suka yaba da ingancin layukan dogo masu hade Sin da kasashen Turai, da ma kasashen da ke aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”. Bugu da kari, sun yi fatan kara hada manyan tsare-tsaren raya kasa, tare da zurfafa hadin gwiwa a sassa daban daban. (Tasallah Yuan)