Hukumar tarawa da rarraba kudin haraji ta kasa ta ce ta kammala shiri domin sake duba albashin masu rike da mukaman siyasa, da ma’aikatan shari’a, domin dacewa da halin da kasar ke ciki.
BBC ta rawaito cewa, wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce a yanzu ana aiki ne da dokar da aka tsara tun shekarar 2008, wadda ta yi la’akari da yanayin da ake ciki lokacin da aka tsara dokar.
- Buhari Ya Bai Wa Ministan Ruwa Wa’adin Wata 3 Don Kawo Karshen Ambaliyar Ruwa A Nijeriya
- Zan Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Kamar Yadda Buhari Ya Yi – Tinubu
Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Engr. Elias Mbam na cewa za su sake duba albashin zababbun shugabanni da masu rike da mukaman siyasa, kama daga shugabannin kananan hukumomi da kansiloli, da gwamnoni da kwamishinoni, da kuma albashin shugaban kasa da mataimakinsa da kuma ‘yan majalisun jiha da na tarayya.
Mista Mbam ya ce hakkin hukumar ne ta tsara albashin zababbun shugabanni da masu rike da mukaman siyasa, tun daga matakin kananan hukumomi da zuwa matakin tarayya.
Haka kuma sanarwa ta ce aikin hukumar ya shafi zababbu da masu masu rike da mukaman siyasa, ban da albashin sauran ma’aikatan gwamnati, wanda hukumar ta ce ke hannan ma’aikatar tsara albashi ta kasa.