Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce; tabbas, ba tare da wata shakka ba, gwamnati za ta biya malamai 3000 hakkokinsu.
Gwamna Sule ya bayyana haka a lokacin da ya ke rantsar da sababbin kwamishinoni a ranar juma’a da ta gabata.
- Yadda Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Ta Gudanar Da Tantance Sabbin Kwamishinoni
- ‘Yansanda Sun Cafke Wani Ɗalibi Da Ya Kashe Abokinshi Da Gatari A Nasarawa
Gwamna Abdullahi Sule ya ce, abubuwan da muka shirya yi shi ne, za mu dauki mataki na tabbatar da cewa mun kawo wata hukumar da za ta tantance malamai 3,000 da suka samu aiki, sannan mu zaɓi nagartattun cikinsu 1,500 don zama malamai na dindindi.
“Sai dai abu guda daya da na yi alkawarin za mu ga dukkan malamai 3,000, duk aikin da suka yi Gwamnatin jihar Nasarawa za ta biya su yadda ya kamata, domin ba laifinsu ba ne da suka samu kansu cikin wannan hali.
Idan ba mu iya samun 1,500 daga cikinsu ba, sai mu fara duba wasu daga wajen ” – Gwamna Sule
Ya zuwa yanzu gwamnatin jihar ta rushe Jagororin TSC, Wanda suka yi almundahana da cuwa-cuwa wajen daukar malamai da gwamnati ta bukaci 1500 su kuma suka dauki 3000 ta barauniyar hanya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp