Babban Jami’in Gudanarwar na Kamfanin Albarkatun Mai ta Kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, ya sanar da shirye-shiryen sake komawa kan ayyukan mai a kogin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe, ya sha alwashin cewa aikin binciko mai a arewa zai ci gaba gadan-gadan.
LEADERSHIP Hausa ta yi tilawar cewa a ranar Talata 22 ga watan Nuwamban 2022 ne shugaban kasa a wancan lokacin, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da aikin fara hako mai a kogin Kolmani, lamarin da ke nuni da karo na farko da aka fara aikin hako mai a yankin arewacin Nijeriya.
- Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe
- Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci
Da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Litinin, Ojulari ya roki al’umman yankin da su kwantar da hankalinsu yayin da ya bayar da tabbacin cewa aikin ci gaba da hako mai din zai ci gaba da gudana.
A cewarsa, “Za mu ci gaba da hakar mai a Kolmani da sauran wurare, bayan aikin hakar mai, mun kuma himmatu wajen kammala aikin bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano.”
Ya kara da cewa wadannan ayyukan za su bayar da damar farfado da kamfanonin da suke rufe ayyukansu a baya da kuma sake ba da damar kirkiro wasu sabbi.
“Wannan ci gaban zai kyautata da inganta ga tattalin arzikin yankin, wanda zai daukaka kowa ta hanyar wadata kowa. Don haka dole ne mu koma wurin kuma mu ci gaba da aikin,” in ji Ojulari.
Dangane da rashin jituwar da ke ci gaba da faruwa a tsakanin NNPCL da rukunin kamfanonin Dangote, sabon shugaban ya ce suna ta kokarin ganin an kawo karshen duk wata rashin jituwa.
“Dangote ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba wanda ya cancanci yabo. Muna kan tattauna yadda za a kawo karshen rigimar. Nan gaba, za mu yi aikin hadin gwiwa domin tabbatar da samar da wadataccen mai ga al’ummar Nijeriya,” in ji shi.
Ya nuna cewa ta hanyar zaman sulhu za su kawo karshen matsalar, “Nan gaba kadan ba za ku ji wata rigima tsakanin NNPCL da matatar mai ta Dangote ba. Za mu yi aikin hadin guiwa domin amfanuwar ‘yan kasa.”
Ojulari ya kuma yi tsokaci kan faduwar farashin danyen mai a duniya a baya-bayan nan, wanda ya rage kudaden shiga da ake sa ran Nijeriya za ta samu.
“Wannan raguwar ta shafi kasafin kudin Nijeriya tun da babban bangarenta ya dogara ne kan kudin shigar mai,” in ji shi.
Sai dai ya bayyana cewa kamfanin na NNPC yana kokarin rage kudin gudanar da aiki domin cin gajiyar abin da suke samu daga siyar da mai da iskar gas.
Da yake mayar da martani ga koke-koken jama’a na cewa farashin man fetur na cikin gida ba ya raguwa ko da farashin duniya ya fadi, Ojulari ya bayyana cewa dillalan na bukatar lokaci don daidaitawa.
“Idan sun sayi man fetur a farashi mafi girma kafin faduwar, za su bukaci sayar da wannan tsohon farashin. Amma tare da sababbin sayayya a farashin kananan, muna sa ran farashin gida zai nuna canji,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp