Gwamnatin Kano ta ce za ta ba za ta ɗagawa kowa kafa ba muddin aka sa me shi da laifin cin hanci da rashawa, inda ya buƙaci hukumar da ta ci gaba da gudanar da aikinta ba sani ba sabo.
Gwaman Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka yayin taron yaƙi da cin hanci da rashawa da hukumar karbar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa, (PCACC), ta shirya albarkacin ranar yaƙi da cin da rashawa ta Duniya da ta gudanar a ranar Talata.
- Yaƙin Gaza Ya Kusan Zuwa Ƙarshe – Amurka
- Kano Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Miƙo Mata Rabonta Na Tsawon Shekaru 25 Daga Shirin NLNG
A cewar Gwamna Abba, cin hanci da rashawa na daya daga cikin abubuwan da ke dakile ci gaban Kowace alumma, wanda dalilin haka gwamnatinsu za ta ci gaba da baiwa PCACC, goyon baya don dakile cin hanci da rashawa a fadin JIhar.
A nashi ɓangaren Shugaban hukumar PCACC, Munyi magaji Rimin Gado, ya ce suna shirya taron duk shekara don tunatar da al’umma kan ranar yaƙi da cin hanci ta Duniya, tare da wayar da kai game da illar da ke tattare da cin hanci da rashawa.
Munyi magaji, ya yaba wa Gwamnan Abba Kabir Yusuf, bisa rashin sanya baki kan yadda ke gudanar da harkokinta na yau da kullum da ma goyon bayan da yake bata inda sauran masu ruwa da tsaki da suka haɗa da jami’an hukumar EFCC da ICPC da dai sauransu suka tofa nasu albarkacin bikin.