ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Aikin Titi A Jihar Ribas

by Sulaiman
2 years ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba wa ƙoƙarin Gwamna Siminalayi Fubara kan ayyukan raya ƙasa daban-daban a Jihar Ribas.

Gwamna Lawal ya kasance babban baƙo na musamman a wajen ƙaddamar da aikin titin da gadojin Opobo, wanda ya gudana a ranar Litinin a ƙaramar hukumar Opobo/Nkoro.

ADVERTISEMENT
  • Za A ƙarfafa Gyare-gyaren Tsarin Tattalin Arziki Da Gwamnatin Tinubu Ke Yi A 2025 – Minista
  • Ministan Harkokin Wajen Sin Wang Yi Ya Lashi Takobin Zamowar Kasar Sin Ginshikin Zaman Lafiya Da Hadaka

Da yake gabatar da jawabinsa a wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa kammala aikin titin Opobo da gadoji ya nuna yadda Fubara ke da himma wajen bunƙasa ababen more rayuwa da inganta zamantakewa da tattalin arziki da jin daɗin al’ummar jihar Ribas.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

“Ci gaban ababen more rayuwa, kamar yadda muka sani, wani ginshiƙi ne na ci gaban tattalin arziki da ci gaban al’umma. Hanyar Opobo da tare da gada babu shakka za ta ƙara samar da haɗin kai, inganta kasuwanci, da sauƙaƙe samun dama ga muhimman ayyuka ga mazauna Opobo da kewaye.

“Samar da ingantattun hanyoyin sufuri zai haifar da ayyukan tattalin arziki da kuma buɗe sabbin damarmaki ga al’ummomi a ciki da wajen jihar. Ingantattun ababen more rayuwa tabbas za su jawo hannun jari, da bunƙasa yawon buɗe ido, da ɗaga darajar al’ummar Opobo a idon duniya”

Gwamna Lawal ya ci gaba da nanata cewa Gwamna Fubara ya jajirce wajen ganin gwamnatinsa ta kawo sauyi ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a jihar Zamfara.

“Muna da ra’ayi ɗaya cewa ingantattun ababen more rayuwa su ne ginshiƙi wajen raya ayyukan tattalin arziki da kuma ɗaukaka matsayin rayuwar jama’armu. A Zamfara, muna samun ci gaba mai ban mamaki ta hanyar ginawa da kuma gyara wasu muhimman ayyuka a faɗin jihar.

“Filin jirgin sama na Gusau da ke gudana, da kuma gina babbar hanyar sadarwa ta karkara da birane, shaida ne ƙarara kan burinmu na ingantawa da kuma zamanantar da muhimman ababen more rayuwa don inganta rayuwar al’ummarmu. Waɗannan ayyukan sun daidaita tare da hangen nesa namu don ƙirƙirar dama da kafa tushe mai ƙarfi don samun ci gaba mai ɗorewa.

“Ina yaba wa Gwamna Fubara bisa jajircewarsa na ci gaban jihar Ribas. Wannan sadaukarwar da ya yi don samar da makoma mai kyau ga jama’arsa abu ne mai ban sha’awa da gaske kuma abin koyi ne ga sauran jihohi.

“Har ila yau, ina gode masa saboda karramawar da aka yi min na kasancewa cikin wannan gagarumin taron. Ina da yaƙinin cewa hanyar Opobo da gadoji za su kawo wa al’ummar Opobo alfanu mai ɗorewa tare da ba da gudummawa sosai ga ci gaban jihar Ribas baki ɗaya.”

Tun da farko Gwamna Siminalayi Fubara ya nuna jin dafinsa ga Gwamna Lawal bisa amsa gayyatar da aka yi masa na zama babban baƙo.

Gwamna Fubara ya bayyana cewa gwamnatin da ta gabata ta ƙaddamar da aikin gina titin zobe na Opobo da gadoji a ranar 28 ga Mayu, 2023. “Mun ɗauki nauyin sake fasalin aikin tare da ɗaukaka shi zuwa matsayin da yake a yanzu. Wannan aikin yana da muhimmanci a gare ni, kuma na yi farin cikin ƙaddamar da shi.”

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030
  • Sulaiman
    Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara
  • Sulaiman
    Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

MASU ALAKA

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027
Labarai

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

July 16, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Manyan Labarai

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai
Siyasa

Ba Zan Iya Jure Halayen El-Rufai Ba Shi Yasa Na Fice Daga ADC – Salihu Lukman

July 16, 2026
Next Post
Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Tarayya Za Ta Tsawaita Kasafin 2024 Zuwa Watanni 6 – Akpabio

Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Tarayya Za Ta Tsawaita Kasafin 2024 Zuwa Watanni 6 – Akpabio

LABARAI MASU NASABA

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

July 16, 2026
Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 16, 2026
Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

July 16, 2026
Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

July 16, 2026
Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

July 16, 2026
Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

July 16, 2026
Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

July 16, 2026
Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

July 16, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

July 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.