Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta bayyana cewar gwamnatin tarayya za ta daina biyan kudin tallafin man fetur a watan Yunin 2023.
Zainab, ta bayyana haka ne a lokacin da ta gana da manema labarai a Abuja, babban birnin tarayya bayan kammala taron tattalin arziki na kasa karo na 28.
- Kayayyakin Masarufi Sun Yi Tashin Gwauron Zabi Da Kashi 21.09
- Sojoji Sun Kashe Shugabannin ‘Yan Bindiga Buzu, Ganai Da sauransu A Harin Jirgin Yaki
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya rawaito cewa biyan tallafin kudin man fetur ya lashe Naira tiriliyan 2.565 tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2022.
Har wa yau, kuma a cikin kasafin kudin bana, gwamnatin tarayya ta kiyasta za ta kashe Naira tiriliyan 3.3 wajen biyan tallafin man fetur din tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2023.
Ta kara da cewa kudin tallafin man fetur din na kawo wa kasafin kudin gibin da dole sai an ciwo bashi kafin cike shi.
“Ba kudi ne da muke da su a hannu ba, kudi ne da muke karbo bashinsu domin biyan tallafin.
“Wasu kasashe sun fara biyan tallafi saboda annobar Korona da batun yakin Ukraine, to amma suna amfani da kudadensu wajen biyan tallafin, to amma mu bashi muke karbowa domin biyan tallafin, to kun ga duka biyu ke nan, don haka dole mu dakatar da shi”, cewar Zainab.
An jima dai ana kai ruwa rana kan takaddamar janye tallafin man fetur a Nijeriya, lamarin da ya sanya ‘yan kasar nan da dama tada jiyoyin wuya.