Sabon babban sufeton ‘yansandan Nijeriya, Olukayode Adeolu Egbetokun ya kaddamar da abin da ya kira tsare-tsaren aiki don farfado da darajar ‘yansanda a idon jama’a.
Babban sufeton ya kaddamar da sabbin manufofin ne yayin wani taron kaddamar da salon shugabancinsa a hedikwatar ‘yansanda da ke Abuja.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’addar ISWAP 6 A Borno
- Mutum 2 Sun Shiga Hannu Kan Fashin Katin ATM A Kaduna
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce a cikin manufofin babban sufeton akwai kafa jami’an kai dauki cikin hanzari mai taken ‘Quick Intervention Squad’ wanda zai hadar da ‘yansandan kwantar da tarzoma da za su kasance shiri don kashe wutar fitintinu da aikata laifuka.
Ya kuma ce shugaban zai tabbatar da aiki da fasahohin zamani kamar kididdigar alkaluma da harkokin tattara bayanan sirri don bunkasa kwazon ‘yansanda.
Haka kuma, babban sufeton zai tabbatar da aiki da wani tsarin martabawa da ba da lada don kara kwazo da karfafa gwiwar jajirtattun jami’an rundunar.
Yayin taron na ranar Juma’a manyan jami’an ‘yansandan Nijeriya daga fadin kasar nan ne suka halarta.