Hukumar Kula da Birnin Tarayya, Abuja, ta gargadi mabaratan da ke bara a gefen titi da su fice daga birnin ko jami’an tsaro su kama su.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ne, ya bayyana hakan a unguwar Katamfe yayin kaddamar da aikin hanyar da ta shiga sabon rukunin alkalai.
- Yadda Dortmund Ta Barar Da Garinta A Santiago
- Kasar Sin: Tsohuwar Kasa, Mai Jagorantar Zamanantar Da Duniya
Ministan, ya koka da cewar yawan mutanen da ke rayuwa a gefen titi yana barazana ga tsaro a Abuja.
Ministan, ya kuma bai wa mutanen da al”amarin ya shafa wa’adin zuwa ranar 27 ga watan Oktoban da su fice daga birnin.
Ministan, ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da rukunin gidajen alkalai 40 a birnin tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp