Gwamnatin Kano ta ce ta himmatu wajen farfaɗo da cibiyoyin masana’antun ɗinki da tsohon gwamna jihar Sanata Rabiu Kwankwaso, ya samar wanda gwamnatin baya ta yi watsi da su.
Kwamishinan ƙananan hukumomi, Mohammed Tajo-Othman, ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, inda ya nuna damuwarsa game da yadda cibiyoyin suka lalace a faɗin jihar.
- Za A Kammala Aikin Titin Abuja-Kaduna-Kano Cikin Watanni 14 – Gwamnati
- Ƴansanda Sun Gano Motoci 2 Da Aka Sace A Kano
Ya ce gwamnatin da ta gabata ta yi watsi da cibiyoyin, wanda aka samar domin horar da al’umma kan sana’o’in dagaro da kai da zummar bunƙasa tattalin arziƙin jihar.
Mohammed, ya jaddada aniyar gwamnatinsu na farfafo da dukkan masana’antun tare da ƙarfafa gwuiwar al’ummar ƙananan hukumomi 44 na jihar kan cewa za su amfana da su.
Kwamishinan ya bayyana cewa manufar aikin ita ce samar da ayyukan yi ga matasan a jihar Kano, ta yadda ba sai sun jira gwamnati ta ba su aiki ba da kuma ƙarfafa tattalin arziki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp