Majalisar Koli Kan Harkokin Shari’a ta Nijeriya (NJC), ta ce za ta gudanar da bincike kan takardun hukuncin zaben gwamnan Kano da kotun daukaka kara da ke Abuja ta fitar.
Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu jami’an majalisar shari’ar suka kai ziyara ofishin Daily Trust da ke Abuja.
- Al’ummar Jihohi 9 Na Arewacin Nijeriya Sun Gamsu Da Shirin ‘New Incentives For All’
- Zaben 2023: NNPP Ta Ci Zabe Ta Hanyar Magudi A Kano – Doguwa
An shiga rudani kan takardun hukuncin shari’ar da kotun daukaka karar da ke Abuja ta fitar na shari’a tsakanin gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna.
A hukuncin da kotun ta sanar ta soke zaben Abba Kabir na jam’iyyar NNPP tare da tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023.
To sai dai bayan fitar da takardun hukuncin, sai wani bangare na takardun ke nuna cewa Abba Kabir Yusuf na NNPP ne ya yi nasara a hukuncin.
Hakan ya haifar da cece-kuce mai tarin yawa a ciki da wajen jihar, tare da jefa shakku a zukatan jama’a.
To sai dai cikin wata sanarwar da magatakardar kotun daukaka karar, Umar Mohammed Bangari, ya fitar, ya ce ya amince da kuskure a cikin takardun hukuncin da kotun ta fitar, to amma ya jaddada sahihancin hukuncin da kotun ta zartar.
Majalisar shari’ar ta ce ta karbi Korafe-korafe da suka shafi shari’ar, inda ta yi alkawarin za ta duba lamarin tare da yin abin da ya dace kamar yadda doka ta tanadar.