A ranar Lahadi 30 ga watan Nuwamban 2025 ne mai Martaba Sarkin Mubi ta Jihar Adamawa, Dr. Alhaji Abubakar Isa Ahmadu ya tabbatar wa da Sanata Dr Abdulrahaman Buba Kwacham sarautar Sarkin Fulanin Mubi. Tabbatar da sarautar ya samu sa albarkan Gwamnan Jihar Adamawa Hon. Dr Ahmadu Umaru Fintiri.
Taron tabbatar da sarautar ya gudana ne a unguwar Zone 7 da ke Abuja babbar birnin tarayya Abuja. Inda wasu manyan fadawar masarautar Mubi suka gabatar wa da Sanata Buba Kwacham wasikar nadin.
- Ƴansanda Sun Kama Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
- Real Madrid Ta Shiga Halin Damuwa Bayan Wasanni Uku Ba Tare Da Nasara Ba
A cikin jawabinsa bayan miqa masa wasiqar, Sanata Abdulraham Buba Kwacham ya gode wa Sarkin Mubi Dr. Alhaji Abubakar Isa Ahmadu da kuma gwamnan Jihar Adamawa Hon. Dr Ahmadu Umaru Fintiri a kan yadda suka amince da bashi wannan mukamin, ya kuma yi alkawarin gudanar da ayyukan da ke tattare da dukaka darajar masarautar ba tare da nuna bambancin qaliba ko addini ba.
Ya kuma bayyana cewa, zai yi aiki tukuru domin ganin an samu zaman lafiya a duk inda ake samun matsaloli da Fulani, ya ce, Fulani mutane ne masu son zaman lafiya da kaunar al’umma, a kan haka ya nemi gwamnati ta yi kokarin samar wa al’ummar Fulani ababen more rayuwa a duk inda suke, “Kamar makarantu, asibitoci da magungunan dabbobisu”.
A kan matsalar tsaron da ake fuskanta a sassan qasar nan, ya ce, al’amari ne da yake bukatar hada hannu ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba, “Lamarin tsaro abu ne da ya shafi kowa da kowa, ya kuma yi alkawarin tabbatar ana yi wa Fulani adalci musamman na ganin an dawo da hanyoyin da shanu ke zirga-zirga (LABI) a shekarun baya, hakan zai rage tashin hankali a tsakanin makiyaya da manoma a qasar nan” in ji shi. Ya kuma yi alkawarin hada hannu da gwamnati don kawo karshen matsalar tsaro a Kawar nan. A jawabinsa na maraba da baki, Hon Ahmad Sajo Geela ya mika godiya ga Masarautar Mubi da gwamnan Jihar Adamawa a kan sarautar da ta ba Sanata Abdulraham Kwacham, ya bayyana cewa, yana da yakinin cewa, Sabon Sarkin Fulanin Mubi zai yi abin da ya kamata musamman ganin cewa, mutum ne mai son mutane kuma kofarsa a buxe take ba tare da nuna banbanci ba. Ya yi addu’ar Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka dora masa.














