A ci gaba da nuna goyon baya ga rundunar sojan Nijeriya wajen dakile aikata duk wani nau’in aikata miyagun ayyuka, kungiyar maharba da tsaron dazuka ta Kasa (NHFSS), reshen jihar Adamawa, ta bayyana bayar da guduwa ga rundunar soji ta 23 da ke Yola.
Malam Aminu Hammanjoda Furo, shugaban kungiyar ya bayyana haka ranar Juma’a, lokacin da ya ziyarci Kwamandan rundunar ta 23 da ke Yola, Birgediya Janar Paul Kefas Zawaya, a hedikwatar rundunar.
- ‘Yan Bindiga: Gwamna Dauda Ya Kai Ziyarar Jaje A Zurmi Da Birnin Magaji
- Kudurin Kirkiro ‘Yansandan Jihohi Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Zauren Majalisa
Furo ya ci gaba da cewa “an kafa kungiyar tsaron ne domin inganta zaman lafiya da tsaron al’ummar Adamawa, musamman a yankuna, lungu da sakon jihar.
“A shirye kungiyar mu take na bada goyon baya ga rundunar soji ta 23, ta hanyar bayanan tsaro akan lokaci wanda zai taimaka wajen daukan mataki akan lokaci, domin fatattakar ‘yan ta’addan da ke amfani da dazuzzuka a matsayin maboyarsu bayan sun aikata miyagun ayyuka” inji Furo.
Da yake maida kalami Kwamandan rundunar soji ta 23 da ke Yola, Birgediya Janar Paul Kefas Zawaya, ya yaba da ayyukan ‘yan kungiyar mafarautan, inda ya tabbatar da goyon rundunar soji ga kungiyar, “rundunar soji ta 23 ta himmatu wajen tuntubar juna don samar da hadinkai da daidaikun mutane, kungiyoyi domin isar da sakon zaman lafiya ga al’umma” inji Zawaya.
Haka kuma shugaban rundunar soji ta 23 da ke Yola, ya yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, bisa kokarin ganin kungiyar mafarautan na aikin taimakawa jami’an tsaro, a yaki da duk nau’in miyagun laifuka a jihar.
Kwamandan rundunar sojin ya kuma bukaci ‘ya’yan kungiyar maharban da su kasance masu taka tsantsan da kwatanta adalci da kiyaye cin zarafin mutanen da ba su ji ba su gani ba lokacin gudanar da aiki