Shugabannin jam’iyyar PDP na kasa sun bayyana damuwarsa kan yiwuwar mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya daya tilo, inda suka bayyana cewa za su kalubalanci duk wani yunurin jam’iyyar APC mai mulki kan mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya daya gabanin zaben 2027.
Jam’iyyar PDP ta bayyana hakan ne a lokacin da take jawabi ga shugabannin jam’iyyar na Jihar Akwa Ibom da magoya bayanta da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar yayin ziyarar godiya ga Gwamna Umo Eno ya kai ofishin jam’iyyar.
- Bajintar Aiki: Majalisar Dattawa Ta Jinjina Wa Ministan Yaɗa Labarai
- Hisbah Ta Yi Kakkausan Gargaɗi Tare Da Kira Ga Iyaye Kan Kula Da Yara Bayan Samun Gawar Wasu 4
Shugabar mata ta jam’iyyar PDP ta kasa, Hajiya Amina Darosimi, wacce ta yi magana a madadin kwamitin gudanarwa na kasa, ta lura da irin ci gaban da gwamnatin Gwamna Eno ta samu, inda ta tabbatar da cewa jam’iyyar ta amince da wannan nasarar.
Da take yaba nasarorin da gwamna ya samu a cikin watanni 19 da suka gabata, Darosimi, ta lura da irin kokarin da aka yi wajen gina jihar a karkashinsa. Tana mai bayyana cewa jam’iyyar na alfahari da irin nasarorin da gwamnan ya samu.
Shugabar matar ta ba da tabbacin cewa, “PDP ta ci gaba da jajircewa wajen yin tir da duk wani yunkuri na mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya daya, domin PDP na bayar da ingantacciyar adawa a cikin al’ummar kasar nan,” kuma ta yi alkawarin goyon bayan jam’iyyar don ganin Gwamna Eno ya samu nasarar lashe wa’adi na biyu. “
Da yake mayar da martani, gwamnan ya nuna jin dadinsa ga jam’iyyar wajen shi ne goyon baya a bangarori daban-daban domin samun nasarar gwamnatinsa tun ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Ya bayyana cewa ziyarar tasa ta yi daidai da al’adar shugabannin jam’iyyar PDP, inda ya ce jam’iyyar ita ce ta mallaki gwamnatinsa.
Gwamna Eno ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da habaka muradun al’amma domin biyan bukatun jam’iyyar da kuma dorewar farin mutanen Jihar Akwa Ibom.
Gwamna Eno ya ci gaba da bai wa jam’iyyar PDP aminci da suka samu damar yin aiki a gwamnati a bangarori daban-daban da su yi kokarin tabbatar da kyakkyawar alaka da jama’arsu ta yadda za su bunkasa kimarsu ta siyasa a tsakaninsu, wanda hakan zai sa jam’iyyar ta amfana a wajen dorewar shahararta.
Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Elder Aniekan Akpan ya gode wa gwamnan kan ziyarar sabuwar shekara da kuma goyon bayan da yake bai wa jam’iyyar.
Ya kuma mika kudirin jam’iyyar PDP na amincewa da Fasto Eno a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2027 a Jihar Akwa Ibom.