Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar wa al’ummar kasar cewa, za a yi jana’izar shugabannin ‘yan ta’adda da ke barazana ga al’ummar Nijeriya a shekarar 2025.
Hedikwatar tsaro ta kuma bayyana dan bindiga, Bello Turji a matsayin “Gawa da ke tafiya da kafafu.”
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabin Murnar Shiga Sabuwar Shekara Ta 2025
- Dabaru Irin Na Sin A Kan Daidaita Harkokin Duniya A 2024
LEADERSHIP ta labarto cewa, Turji a wani faifan bidiyo na baya-bayan nan, ya bukaci fafatawa da sojoji.
Turji ya kuma bukaci a sako wani dan ta’addan da sojojin Nijeriya suka kama mai suna Baka Wurgi, tare da yin barazanar kai muggan hare-hare a kan al’ummar Zamfara a 2025 idan sojoji suka ci gaba da tsare Wurgi.
Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, da yake mayar da martani ga faifan bidiyon a takaitattun bayanan karshen shekara a ranar Talata, ya ce, ba zai yi cacar baki da Turji ba, amma ya sha alwashin cewa, za a kawar da Turji kamar yadda aka kawar da sauran kwamandojin da suka gabace shi.